Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, kan takaddamar jirgin saman Nigeria Air.
An tattaro cewa Sirika ya isa hedikwatar DSS da ke Abuja domin amsa tambayoyi game da cece-kucen da aka yi na kaddamar da jirgin.
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Bashir Zuntu A Matsayin Babban Akanta Na Jihar Kaduna
- Gwamman Zamfara Ya Karrrama Hajiyar Da Ta Tsinci Dala 80,000 A Saudiyya
A cewar SaharaReporters, Sirika ya isa hedikwatar da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis a cikin wata mota kirar Range Rover Sport Utility Vehicle (SUV).
DSS ta gayyaci Hadi Sirika domin amsa tambayoyi.
Idan za a tuna cewa a watan Mayu gwamnatin Muhammadu Buhari ta kaddamar da wani jirgin Boeing 737-800 na kamfanin jiragen saman Habasha a matsayin jirgin saman Nigeria Air.
Bayan kaddamar da jirgin, mukaddashin Manajan Daraktan Kamfanin, Captain Dapo Olumide, ya bayyana cewa jirgin ya haura shekaru 10, kuma mallakin kamfanin jiragen saman kasar Habasha ne.
Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya.