Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta karyata rahoton da ke cewa jami’anta sun kama daya daga cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar na 2023.
Sanarwar ta DSS ta biyo bayan zargin da babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature, ya yi, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano na da tabbacin kame alkalan da suka gudanar da hukuncin zaben na ranar 18 ga watan Maris.
- DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Kori Gwamna Abba Gida-Gida Ta Tabbatar Da Nasarar Gawuna
- NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara
Yayin da yake zantawa da PRNigeria ta wayar tarho, kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya musanta wannan zantukan na mai magana da yawun gwamnan Kano.
Afunanya ya ce: “Wannan magana ce ta ban dariya, kama alkalai saboda wane dalili? Ba gaskiya ba ne gaskiya.”
Idan dai za a iya tunawa, a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, yace, “babu dalilin da zai sa hukumar ta DSS za ta kama alkali ba tare da wata tuhuma ba,
“Hatta wannan hukunci da suka zartar, ba mu san daga ina suka fitar da shi ba, wata kila sun yanke hukuncin ne bisa tursasawa duk da dai ba ni da tabbas, ba mu san inda suka yanke hukuncin ba, kawai dai muna iya ganinsu akan allo.”
“Abubuwa da yawa sun faru a bayan fage, abin kuma ya ba mu mamaki, wanda aka ce shi ne ya lashe zaben, bai ma shiga cikin lamarin karar ba, Gawuna ya tsaya takara ya amince da shan kaye, kuma ya taya Abba Kabir murna, ya ce ba zai je kotu ba.” Cewar Dawakin Tofa