Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya, DSS ta shigar da tuhume-tuhume biyar da suka shafi ta’addanci kan dan fafutukar kare hakkin al’umma, mazaunin Kaduna, Mahdi Shehu biyo bayan wani rahoto da ya wallafa a shafinsa na yanar gizo.
An shigar da karar ne a babbar kotun tarayya da ke Kaduna a ranar Juma’ar da ta gabata, kwanaki biyu bayan da Jami’an DSS suka sake kama shi a asibitinsa da ke Unguwar Dosa.
- Ƙasashe 7 Sun Mara Wa Nijeriya Baya Don Kafa Cibiyar Koyar Da Ilimin Yaɗa Labarai Ta UNESCO – Minista
- An Kashe Na Biyun Turji A Shugabanci Tare Da Fitattun Kwamandojin ‘Yan Bindiga A Zamfara
LEADERSHIP ta rahoto cewa, a watan Disambar 2024, an kama dan gwagwarmayar tare da gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin yada wani faifan bidiyo da aka ce bai tabbata ba a kafar sada zumuntarsa.
DSS ta bayyana cewa, an kama Shehu ne bayan ya yada “Bidiyon karya da ke nuna cewa, gwamnatin Nijeriya ta bai wa Faransa izinin kafa sansanin soji a Arewacin kasar.”
Daga baya babbar kotun jihar Kaduna ta bayar da belinsa a ranar 9 ga watan Janairun 2025 a kan kudi har naira miliyan 3 sannan kuma dole wasu manyan malamai guda biyu su tsaya masa.
Sai dai, sabon matakin da DSS ta dauka ya zo ne kwana guda bayan da ta shigar da kara a gaban kotun tana neman a bata damar tsare Shehu na tsawon kwanaki 60.