ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jagoranci Nagari: Kungiyar Lauyoyi Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo

by Sulaiman
2 years ago
Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa tabbatar da doka da oda na buƙatar ƙwarewa ta fasaha, jajircewa da kuma gaskiya da riƙon amana.

Gwamna Lawal ya kasance babban baƙo a wajen taron shari’a na shekara-shekara ta 2024 da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA) reshen Gusau ta shirya.

ADVERTISEMENT
  • Saudiyya Ta Ware Dala Biliyan 100 Don Sabunta Masallatan Harami
  • Sin Da AU Sun Cimma Nasarori A Fannonin Diflomasiyya Da Tattalin Arziki

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa a yayin taron, gwamna Lawal ya samu lambar yabo ta karramawa a matsayin babban abin tunawa kuma mutum mai tasiri ga al’ummar jihar Zamfara.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

Ya ƙara da cewa, shugaban NBA reshen Gusau Mu’azu Shehu Ahmad Esq ne ya ba gwamnan lambar yabon.

A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa taro kamar na NBA yana ƙara ƙwarin gwiwa ga ƙwararrun lauya don musayar ra’ayoyi da inganta samar da adalci, dimokuraɗiyya, da bin doka.

Ya ce, “Taken taron na bana shi ne; “Tabbatar da Doka: Ginshiƙin Ci gaban Dimokraɗiyya”. Yana nuna da irin rawar da fannin shari’a ke takawa wajen tsara al’ummarmu ta hanyar tabbatar da kyawawan ɗabi’u, adalci da riƙon amana.

“Ina da yaƙinin cewa za mu iya ƙarfafa ginshiƙin dimokuraɗiyyar mu da kuma ginshiƙin wanzuwar mu a matsayin al’umma ta hanyar sadaukar da kai ga bin doka da oda.

“A halin da ake ciki, ina yaba wa Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya reshen Gusau, bisa namijin ƙoƙarin da suke yi na tabbatar da adalci da bin doka da oda. Haƙiƙa sadaukarwar da kuka yi ga wannan aiki mai daraja abin a yaba ne kuma abin koyi ne.

“Ina kira gare ku da ku ci gaba da nuan halin ƙwarai na ma’aikatan shari’a don tabbatar da cewa kun kasance ginshiƙin fata ga talakawa da duk masu neman adalci.

“Na yaba wa ƙoƙarin lauyoyi wajen ganin an yi adalci ba tare da nuna son kai ba cikin gaggawa, har a lokutan da ake fuskantar ƙalubale. Tsayuwarku ta kasance ƙwarin gwiwa kuma ta zama abin tunatarwa cewa adalci shi ne ginshiƙin kowace al’umma mai wayewa.

“Gwamnatin jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Muna aiki tuƙuru don magance matsalolin rashin tsaro da samar da yanayin da al’ummarmu za su zauna ba tare da tsoro ba.

“Ina kuma so in jaddada muhimmancin ilimin shari’a wajen ƙarfafa tsarin adalcinmu.

“Tsarin ilimin shari’a yana buƙatar karatu da haƙiƙa. Ina roƙon ku da ku riƙa amfanar juna wajen da horo da ilimin da ku ka samu, kamar wannan taro na makon shari’a, don kasancewa a sahun gaba wajen aiki da doka.

“A wannan lokaci, ina miƙa godiya ta ga waɗanda suka shirya wannan babbar lambar yabo a gare ni. Jajircewar da na yi na yaƙar rashin tsaro, da bin doka da oda, da gina ababen more rayuwa abin a yaba ne matuƙa.

“Ba abin alfahari ba ne kawai, a’a, shaida ce ga namijin ƙoƙarin da duk waɗanda suka yi aiki tare da ni suka yi wajen gina jihar Zamfara mai tsaro, da adalci, da wadata cikin watanni 20 da suka gabata.

“A ƙarshe, yayin da nake yaba wa Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya reshen Gusau, kan yadda suka saba shirya wannan taron na shekara-shekara, cikin alfahari nake bayyana buɗe makon taron shari’a na 2024. Ina addu’ar shawarwarinku su kasance masu ma’ana da tasiri. Allah Ta’ala Ya yi mana jagora a cikin ayyukanmu baki ɗaya”.

Zamfara
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan
  • Sulaiman
    ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Next Post
Sabon Albishir Ga Masu Kawo Ziyara Ko Yada Zango A Birnin Beijing Na Kasar Sin

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.