• English
  • Business News
Sunday, October 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin

by Rabi'at Sidi Bala
3 weeks ago
in Madubin Rayuwa
0
Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban waɗanda suka shafi al’umma, ciki sun haɗar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba e game da da abin da ya shafi, yawan kwaɗayi da son abin duniya da wasu matan ke yi, inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me ya sa wasu matan suka fiya buri da kwaɗƙyi da jurar wulaƙanci a soyayyar naira, fiye da soyayyar asali da gaskiya?, Me yake janyo hakan?, Ko akwai wasu matsaloli da za a iya fuskanta game da hakan?”. Ga dai bayanan nasu kamar haka;

Sunana Fadila Lamiɗo daga Jihar Kaduna:

Mata

Ai yanzu soyayyar gaskiya ta yi ƙaranci, Saboda mafi yawan mazan basu da amana wulaƙancin da babu a farko yana iya zuwa a ƙarshe, idan zama yayi zama shi ya sa mata suka gwammaci su jure duk wani ƙalubalai in har za a basu kuɗi domin biyan buƙatun su. Shwarata a nan maza su riƙa riƙe amana duk macen da ta aure ka ba kada shi ko da ka samu a ƙarshe ka daraja wannan matar kar ka wofintar da ita, hakan zai sa mata su rage buri da kwaɗayi da gudun wulaƙanci.

Labarai Masu Nasaba

GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija:

Mata

Ni dai a tawa fahimtar mata masu yin hakan manya ne, waɗanda sun riga sun yi aure, su ma mazan su suke zuwa da wannan ‘interest’ ɗin. Wasu kuma da yanayi na rayuwa, wasu suna da ‘ya’ya, da ‘yan’uwa, wasu ba suda abin yi. To, rashin abin yin nan wataran ya kan jaho hakan, mace ta zauna ta yi soyayyar ƙarya sabodƙ kuɗi dan ta taimaki kanta, da ‘yan’uwanta da ‘ya’yanta. Kamar yadda su mazan yanzu ba sa iya bayar da kuɗin sai a soyayyar ƙarya, ba wani abu ne yake janyo hakan ba face rashin abin yi duk wanda yake da abun yi ba zai zauna kwaɗayi da soyayyar ƙarya ba. To, amma rashin abun yi ya yi yawa a zamanin nan dan shi yake janyo haka. Shawara mutum ya dage ya nemi na kansa ya daina tsayawa soyayyar kwaɗayi dan watarana babu irin wulaƙancin da mutum ba zai gani ba.

Sunana Mohammed Isah, Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Abu na farko da duk matar ko budurwar da take irin wannan tunanin ba zai wuce rashin sannun matsayinta ba na cewa Allah ne yake bada kuɗi ko nace naira a duk lokacin da ya ga dama. Sannan soyayar naira bata gaskiya bace duk lokacin da babu kuɗin rabuwa take amma idan akwai gaskiya ko asali tafi karƙo. Abu na biyu dai ba zai wuce son zuciya ba a nawa tunanin. Ai tunda ba Allah ko gaskiya a soyayyar dole a samu matsaloli. Shawara a nan ita ce mace ta yi wa abokin soyayyar riƙo na gaskiya ba don abun hannunsa ba saboda ita ce ginshiƙin zaman aure.

Sunana Princess Fatimah Mazadu, daga Jihar gomben Najeriya:

Mata

Zamani ne kawai na nuna isa da fifiko da izza, kowacce tana so ita ma ace ita wance ce. Ba ta son a sakata a layin talakawa tunda a ganinta talauci ba aji, ga rashin darajawa, gara ta gwammaci duk wani wahala ta sameta, in har za ta fita a kirata ‘yar gata ko maji daɗi a gidan aure ko ‘yan matanci. Abun cewa kam na da yawa, dan abun cike yake da takaici da abun haushi mai tarin yawa, yadda akan son duniya mace ta maida kanta jaka ta wofantar da kanta wurin aikata assha ko bin wasu hanyoyin Dan samun ɗaukaka.

Kwadayi da buri in ka jira kanka arziƙi ruwan fomfone inda rabonka zai zo kanka in ba rabonka Allah zai maka darajar da shi kanshi mai dukiyar baki isa ya tozarta ka ko ya wulaƙanta ka ba, duk wanda ya hau motar kwaɗayi dole ya sauka a tashar wulaƙanci. Shawara ta farko dogaro da kai,ba biyu tawakkali, na uku tsoron Allah da tsoron zubda mutunci. Mace kaɗan zat a aikata mutuncinta ya zube gabaɗaya a idon duniya su kiyaye sosai duk da zamani ake binmake lalacewa da karon buɗi “more especially” wayar salula da ‘competition’ na motoci shi ya gama lalata mataye da yawa da gurbata rayuwarsu. Allah ya mana tsari ya mana maganin talauci da abun da bazamu iyaba,ya Bamu sanaa mu tsare mutuncimu dan gudun wulaƘanci da tozarcin duniya da lahira.

Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos, a Jihar Filato:

Mata

Mata wani jinsin halitta ne da Allah ya halicce su da son jindaɗi, nishaɗi da ado. Ana cewa, mata halitta ne da ke buƙatar kulawa da tattali. Don haka duk inda suka ga za su samu damar cimma wannan burin nasu, ta nan hankalinsu yake karkata. Wannan ba yana nufin dukkan mata suna da son kwaɗayi da abin duniya ba. Amma tabbas nazari ya nuna duk wanda yake so ya ga mace a ainihin yanayin ta na mace to, ya ba ta kulawa yadda ya kamata. Kodayake a ƙoƙarin su na samun jindaɗi da kulawa da biyan buƙata, mata kan nuna wasu halaye na rashin gaskiya, yaudara, da cin amana idan abin ya yi tsanani.

Sannan wannan buri nasu na sa su iya jure duk wani wulaƙanci, da ƙasƙanci, in dai za su samu biyan buƙata. Sau da dama mun sha ganin inda budurwa ta gujewa saurayin da suka daɗe suna soyayya, saboda ta samu wanda ya fi shi kuɗi, ko matsayi, ko yawan hidima, ko da kuwa shi ma yaudararta yake yi. Shi ya sa sau da dama suke ƙarewa cikin takaici da nadama, da zarar sun gane wanda suka bai wa soyayyar su ta gaskiya, shi ba da gaske yake son su ba. Yayin da su kuma ba sa mayar da hankali ga wanda ke son su da gaskiya, idan sun lura buƙatarsu ba za ta biya ba, a tare da shi. Lallai ina ganin ya kamata mata su riƙa zurfafa tunani da nazari sosai kan hanyoyin da suke so su cimma burikansu, ba kowanne lokaci ne kuɗi ke maganin matsala ko cika buri ba.

Wani lokaci soyayyar gaskiya da kyautatawa cikin amana da haƙuri suna da tasiri sosai wajen canza akalar rayuwar mutum, ko da kuwa a zahiri mutum yana ganin babu alamun jindaɗi ko samun nasarar kan abin da yake nema. Soyayyar Gaskiya, da adalci, da riƙon amana, su zama su ne abin dubawa a wajen duk wani abokin zama nagari.

Sunana Hadiza Ibrahim Ɗan Auta Ƙaura-Namoda Jihar Zamfara:

Mata

Ban ga amfanin duk zaman da babu mutunci ba, ballantana uwa-uba soyayya. Amma idan har kwaɗayi da dogon buri mace ta saka a gabanta; to dole ta jure duk wulaƙancin da zai biyo bayan hakan. Saboda ita ma ba soyayyar gaskiya ce take yi wa mai kuɗin ba, dabara ce kawai take yi don ta amfana da shi. Wayo ne kawai ke jawo irin wannan mutuwar zuciya, saboda masu irin halin suna shanye takaicin namiji matuƙar sun san yana da kuɗi. Kuma ba wai don suna da biyayyar ba, ba kuma don ladabin da suke yi na gaske ba ne. Haka ma kalaman wani lokaci duka na ƙarya ne.

Amma matuƙar mace ta san ciwon kanta; ba za ta zauna inda ake ƙoƙarin tozarta ta a kan abin duniya ba. Matsalolin da irin soyayyar take haifarwa suna da yawa, a cikin su akwai; rashin ganin girman yarinyar, rashin ƙima, maganganun da duk suka fito bakinsa zai iya faɗa mata, don yana da tabbacin ba saboda Allah take tare da shi ba. Kuma yana ji a ransa yadda ta so shi a yadda yake saboda kuɗi, ko ya rabu da ita zai samu waɗanda suka fi ta komai, tun da yana makamin riƙe su a hannunsa. Shawarata a nan ɗaya ce, duk runtsi mace kada ta manta ita mai daraja ce, kada kuɗin mutum ya rufe mata ido ta dinga zubar da ajinta na ‘ya mace a kan abin duniya. Don ko an yi auren matuƙar ya saba yi mata abin da ya ga dama, to ba lalle ne ta samu irin nutsuwar da take tunanin samu ga zaman aure a gidan mai kuɗi ba. Saboda ta baro kyawu tun ranar haihuwa, saboda mutunci ya fi kuɗi.

Sunana Idris Haruna Zareku Miga A Jihar Jigawa:

Rashin imani da soyayya ta gaskiya. Wasu mata suna ganin maza da yawa ba su tsayawa a soyayya da gaskiya, don haka sukan zaɓi abin da zai ba su amfani kai tsaye (kuɗi ko gata). Tsoron talauci da rashin tsaro na rayuwa, wasu mata suna ganin cewa, soyayya ta gaskiya kaɗai bata isar da rayuwa mai sauƙi ba. Suna fifita mai kuɗi domin suna tsammanin zai ba su tsaro, jin daɗi da mafita daga matsalolin rayuwa.Wulaƙanci da cin zarafi. Wasu maza masu kuɗi suna amfani da hakan wajen  danniya da wulaƙanta mace, domin suna ganin ana son su ne kawai saboda dukiya. Ku gane cewa kuɗi ba shida tabbatacciyar kariya. Dukiya tana ƙarewa, amma mutunci da soyayya na gaskiya suna iya ɗorewa idan an kula da su.

Sunana Khadija Auwal, Koki A Jahar Kano:

A ganina shirme ne da rashin sanin darajar kai, domin kuwa ai duk wanda yasan darajarsa ba zai bari a hulaƙanta shi ba akan kuɗi, domin kuwa mutunci ya fi kuɗi. Tsantsar san abin duniya ne kawai da kwaɗayi, domin kuwa duk abin da haƙuri da mutunci bai baka ba, to na tabbata rashin haƙuri ba zai baka ba. Tabbas hakan yakan saka wasu su rasa mutuncinsu, sannan kuma su rasa kimarsu ta hanyar yin hakan. Masu aikatawa ya kamata su gane cewar soyayyar Allah da Annabi ita ce soyayyar gaskiya, amman soyayyar kuɗi babu abin da yake cikinta sai wulaƙanci da ƙasƙanci fatan masu aikatawa za su gane illar hakan su daina aikatawa.

Sunana Sunana Hauwa Abubakar Sarki, Garin Suleja Jihar Niger:

Mata

Galibin matan da suke da irin wannan buri da kwaɗayi da kuma jure wulaƙanci a soyayya, ‘ya’yan talakawa ne musamman idan saurayin nasu mai kumbar susa ne. Su nemi abin yi, su nemi sana’ar da taro sisi zai rin’ƙa shigo masu. Hakan zai taimaka masu wajan rage buri da kwaɗayi da kuma sanya ido a kan abun hannun saurayi bare har akai ga sai ya wulaƙanta su kafin ya basu. Talauci da kuma rashin ije kai inda Allah ya ajeka. Matsala na farko daga lokacin da mace ta kasance mai kwaɗayi dole ta zama tana da buri, daga lokacin da mace ta kasance mai dogon buri to fa komai za ta iya aikatawa domin ganin burinta ya cika. Shawarata ga ‘yan’uwana mata shi ne a rage kwaɗayi da dogon buri, sannan kuma a nemi sana’ar yi. Sana’a na toshe ƙofokin ɓarakan rayuwar ɗiya mace. Haka zalika rashin shi kuma na buɗe ƙofokin ɓarakar rayuwar ta, duk macen da take da abin yi bata cika sa’ido da kwaɗayi akan abun hannun wani, bare har a kai ga wulaƙanta ta.

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Jihar Kano:

Hmmm kawai dai son zuciya ne da kwaɗayi da kuma burin ace wane kake soyayya da shi, kai ka isa tunda dama ba soyayyar Allah da Annabi ake yi ba,ta abin duniya ce dole a jure wulaƙaci da duk wasu abubuwa da za su biyo bayan hakan, duk wanda ya hau motar kwaɗayi za ta kai shi tashar wulaƙaci. Abin cewa dai su nutsu su kama kansu.To, ai son abin duniya ne da kwaɗayi da buri, ita fa ta kai, ta cika, ta tambatsa sai manya-manya. Babbar matsalar wani lokacin soyayya ba ta wani ƙarkon kirki. Suyi hakuri su nemi daidai dasu ba sai an nemo babban kai ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AureMataSamariZamani
ShareTweetSendShare
Previous Post

Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin

Next Post

Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

Related

Goron Sallah
Madubin Rayuwa

GORON JUMA’A

2 days ago
Goron Sallah
Madubin Rayuwa

GORON JUMA’A

1 week ago
Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata
Madubin Rayuwa

Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata

2 weeks ago
Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)
Madubin Rayuwa

Shawara Ga Matashin Da Matarsa Ta Samu Juna Biyu (1)

4 weeks ago
GORON JUMA’A
Madubin Rayuwa

GORON JUMA’A

1 month ago
Goron Sallah
Madubin Rayuwa

GORON JUMA’A

3 months ago
Next Post
Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

Kasar Sin Na Samarwa Duniya Damammaki A Fannin Hada-hadar Ba Da Hidima

LABARAI MASU NASABA

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara

October 5, 2025
Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?

October 4, 2025
Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa

October 4, 2025
Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or

October 4, 2025
Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

Jonathan Ya Ƙaryata Batun Danganta Buhari Da Boko Haram

October 4, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

Sin Ta Yi Kira Ga Kasa Da Kasa Su Ki Amincewa Da Takunkumin Bangare Daya

October 4, 2025
Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

Kasar Sin Ta Soki Matakan Harajin Amurka “Na Ramuwa” A WTO

October 4, 2025
Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

Jami’ar Nsukka Ta Ce Shaidar Digirin Ministan Fasaha, Uche Nnaji, Ta Bogi Ce

October 4, 2025
Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

Jami’in MDD: Shawarar GGI Za Ta Jagoranci Duniya Zuwa Samun Kyakkyawar Makoma Mai Cike Da Adalci

October 4, 2025
Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

Nijeriya Ta Samu Kwarin Gwiwar Zuwa Kofin Duniya

October 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.