Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Yobe sun kama wani matashi dan shekara 29 mai suna Joshua Agugu bisa zarginsa da hannu wajen damfarar wadanda ba su ji ba ba su gani ba masu amfani da PoS.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata sanarwa da ya fitar, ya tabbatar da kama Agugu, mazaunin unguwar babbar kotun Gizza Plaza, karamar hukumar Keffi a jihar Nasarawa ta hannun hukumar leken asiri ta SID.
- Yadda Ciniki Ya Habaka Tsakanin Babban Yankin Kasar Sin Da Yankin Macao A Fiye Da Shekaru 25
- Wike Ya Kwace Filin Buhari, Abbas, Akume Da Wasu Mutane 756 A Abuja
A cewar sanarwar, an samu Agugu da katin shaidar sojan ruwan Nijeriya na bogi wanda ya ke amfani da shi wajen damfarar ‘yan kasuwa musamman masu amfani da PoS da masu shaguna.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, CP Garba Ahmed ya bukaci jama’a da su kara yin taka tsantsan tare da yin hattara da masu damfara.