Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma.
Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da al’ummar mazabarta.
- Gwamnatin Edo Za Ta Biya Diyyar Mafarauta ‘Yan Kano 16 Da Aka Kashe A Uromi
- BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa
Amma, ta bijirewa umarnin gwamnati, Natasha ta isa gidanta na Ihima a cikin wani jirgi mai saukar Angulu da misalin karfe 1:00 na ranar Talata, inda dimbin magoya bayanta suka taru a gidanta tun da safiyar karfe 7:00 suna jiran isowarta.
Da take yi wa magoya bayanta jawabi, Natasha ta fara da bayyana farin cikinta na dawowa gida.
“Ina bukatarku duka ku kula da abin da zan fada, gida akwai dadi.
“Na ji daɗi da na dawo gida. Kuma babu wanda zai iya hana ni zuwa gida.
“Ni Ebira ce, Dr. Akpoti mahaifina ne, na san gidana, ni ba mahaukaciya ba ce,” in ji ta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp