• English
  • Business News
Friday, May 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Da Matsin Rayuwa: Bankuna Na Ci Gaba Da Cin Kazamar Riba Ta Hanyar Dora Wa Al’umma Haraji

by Rabi'u Ali Indabawa
3 weeks ago
in Manyan Labarai
0
Duk Da Matsin Rayuwa: Bankuna Na Ci Gaba Da Cin Kazamar Riba Ta Hanyar Dora Wa Al’umma Haraji
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bankunan kasuwanci da wasu kamfanonin kere-kere a Nijeriya sun magance matsalolinsu ta hanyar share fagen samun dimbin riba tare da bayyana ta ga masu hannun jarinsu a shekarar kudi ta 2024.

Sakamakon binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya yi nuni da cewa duk da koma-bayan tattalin arziki da kuma tsadar kayayyaki dake addabar ‘yan Nijeriya a cikin shekarar da ta gabata, tuni yawancin bankuna da kamfanoni suka shawo kan dukkanin wasu matsaloli tare da bayyana dimbin riba, kai har ma da biyan masu hannun jari.

  • Manchester Ta Kai Zagayen Semi Final A Europa Bayan Doke Lyon
  • Yawan Kudaden Da Al’ummun Sin Suka Kashe Kan Kayayyakin Masarufi Ya Kai Yuan Triliyan 12.5 A Rubu’in Farko

Financial edperts and shareholders who spoke with our correspondent edplained that the organisations’ positibe showings arose from fored windfall, as banks found themselbes at the surplus end of policy actions and, hence, realised unprecedented FD windfall and huge income from inbestment in public debt.

Misali, kamfanonin siminti na Nijeiya sun bayyana samun ribar da ta kai Naira biliyan 984.432 kafin haraji, sakamakon karuwar girman arziki da kuma gyare-gyaren farashi.

A bangaren banki kuwa, Bankin Zenith, Guaranty Trust Holding Company, United Bank for Africa, Fidelity Bank, Stanbic IBTC Holdings da Wema Bank sun bayyana ribar Naira tiriliyan 3.41 bayan harajin shekarar 2024, an samu sama da Naira tiriliyan 2.1 a shekarar 2023.

Labarai Masu Nasaba

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

Hakazalika, kamfanoni 43 da aka bayyana sun ba da shawarar raba jimillar Naira tiriliyan 1.678 ga masu hannun jarinsu, tare da yaba wa abokan huldarsu.

A cikin 2024, bangarori na kasuwancin Nijeriya ya gamu da kalubale masu yawa na tattalin arziki da samar da ababen more rayuwa wadanda suka yi matukar tasiri ga ayyukansa. Masana’antun sun fuskanci matsin lamba daga hauhawar farashin kayayyaki, faduwar darajar Naira, hauhawar kudin ruwa, karin kudin wutar lantarki, karancin tallace-tallace, yawan haraji da kuma tabarbarewar tsaro.

A cikin wannan babbana al’amari, kamfanoni a manyan sassan tattalin arziki sun ba da rahoton sakamako mai karfi na kamfanoni da kuma bayar da lada ga masu hannun jari.

Idan za a kimanta halin da ake ciki, babban jami’in gudanarwa (Shugaba) na HighCap Securities Limited, Mista Dabid Adonri, ya ce, “Ta hanyar samar da, bankunan sun sami kansu a karshen ayyuka na wasu manufofi, wanda ta haka ne suka fahimci faduwar canjin kasashen da ba a taba gani ba da kuma makudan kudaden shiga daga zuba jari a basussukan jama’a.

“Abin takaici shi ne, sauye-sauyen kasuwanni da matakan tsare-tsare na kudi wadanda ke samar da karuwar kudaden shiga na bankuna sun sanya yawancin masana’antun da suka dogara da shigo da kayayyaki zuwa cikin gida asara, wadanda babu shakka sun yi nasasar shawo kan lamarin, kamar masu samar da siminti, suna da kasuwancinsu na fitar da kayayyaki domin samun daidaito.”

Ya yi nuni da cewa, duk da rauni na kasuwancin kayan masarufi sakamakon hauhawar farashin kayayyaki, bangaren gwamnati na ci gaba da aiwatar da manyan ayyuka, wadanda ke cinye kayayyakin gini da dama. Don haka ne ribar da kamfanoni kamar Dangote Cement da BUA Cement suka bayyana.

“To kuwa tun da aka riga aka bayyana wadannan kamfanoni a bainar jama’a da kuma yadda tsarinsu yake, babu wani dalili da zai musanta ribar da suke samu a ce ba gaskiya ba ce.

Adonri ya ce “Yawancin kamfanoni na Nijeriya suna yin fatali da ci gaban tattalin arzikin kasar da ke tabarbarewa, suna ba da rahoton riba da kuma yawan kudaden da aka samu,” in ji Adonri.

Babban jami’in gudanarwa na InbestData Consulting Limited Ambrose Omordion, ya aminta da cewa “bankuna da sauran kamfanonin Nijeriya suna bayar da rahoton riba mai yawa da kuma kudaden da ake samu duk da tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma karancin sayayyar kayayyaki.”

Ya lura cewa manyan kamfanoni, musamman a bangaren banki, na iya za su iya tsira daga manyan kalubalen tattalin arzikin da kananan ‘yan kasuwa da daidaikun mutane ke fuskanta.

Ya kara da cewa ” Alal misali, bankuna, na iya samun manyan kudaden shiga daga wasu kwamitoci ko ayyukan sanya hannun jari wadanda ba su da alaka da ainihin kasuwancin ba da lamuni,” in ji shi.

A halin da ake ciki, shugaban Kungiyar Masu Hannun Jari Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (ISAN), Moses Igbrude, ya yi nuni da cewa, “Rabon da bankunan ke bayyanawa gaskiya ne, domin harkokin kasuwancinsu na bayar da hidima ne, wanda ke samar da jari don ciyar da tattalin arzikin kasa gaba.

“Ba tare da manyan kudaden da za a inganta tattalin arzikin kasa ba, to ba za a taba samar da wasu dabaru na farfado da shi ba. Tare da kowane ciniki, akwai farashi da ya shafi sakonnin rubutu zuwa riba akan lamuni da aka ba wa abokan ciniki, kuma hakan na ba da ayyuka da yawa ga abokan cinikinsu a duk fadin kasar,” in ji shi.

A halin yanzu dai, shugaban kungiyar masu Masana’antu ta Nijeriya (MAN), Otunba Francis Meshioye ya yi kira da a tallafa wa bangaren masana’antu.

Ya ce, “ A 2025, fannin masana’antu ya ta’allaka ne ga nasarar sauye-sauyen tattalin arziki da ake ci gaba da samu, wadanda suka hada da aiwatar da sauye-sauyen harajin da ake shirin yi, da daidaita muhimman alamomin tattalin arziki, da zuba hannun jari a fannonin ababen more rayuwa da fasaha.

“La’akari da jerin sauye-sauye na kasafin kudi na gwamnatin yanzu, ana sa ran samun saukin tabarbarewar tattalin arzikin da samun wasu ci gaba a wannan shekara tare da kwanciyar hankali a cikin tsarin musayar kudi a 2025.”

Meshioye ya kara da cewa, domin fannin ya dawo da karfinsa, dole ne a ci gaba da kokarin inganta ayyukan da ake yi da kuma kara yin gasa, domin hakan na da matukar muhimmanci wajen taimaka wa masana’antun Nijeriya su shawo kan kalubalen da suke fuskanta.

Meshioye ya ce, “Masana’antu na da muhimmanci wajen bunkasa da kuma dorewar ci gaban tattalin arzikin Nijeriya. Muna neman gwamnati ta daidaita tare da amincewarmu cewa samun nasarar masana’antu kai tsaye nasara ce ga tattalin arziki, da bin hanyar fadadawa, rayuwa mai kyau ga ‘yan kasa.”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BankunaHarajiMatsin RayuwaRiba
ShareTweetSendShare
Previous Post

Bukatar Kawo Karshen Mamayar Da Kamaru Ke Yi Wa Yankunan Nijeriya

Next Post

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

Related

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje
Manyan Labarai

Farfaɗo Da Mutuncin Nijeriya Ta Hanyar Buɗe Kofofin Kasuwanci Da Ƙasashen Waje

8 hours ago
Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
Manyan Labarai

Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai

9 hours ago
Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa
Manyan Labarai

Man Utd Ta Lallasa Bilbao, Ta Kai Wasan Ƙarshe Na Gasar Europa

17 hours ago
Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma
Da ɗumi-ɗuminsa

Robert Prevost Ya Zama Ba’amurke Na Farko Da Ya Zama Fafaroma

21 hours ago
Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB

22 hours ago
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai
Manyan Labarai

Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra

1 day ago
Next Post
Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (3): Shari’ar Manzon Allah (SAW) Ta Zo Da Wayewa A Kowane Fanni

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya

May 9, 2025
Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Halarci Bukukuwan A Moscow

May 9, 2025
AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 

May 9, 2025
Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

Rabe-Raben Aikin Hajji Da Abubuwan Da Aka Halasta Ga Mahajjaci

May 9, 2025
Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

Matatar Mai: Har Yanzu ‘Kabal’ A Ɓangaren Mai Na Yaƙar Nasararmu – Dangote

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.