Gazawar da Gwamnatin Nijeriya ta saba yi na tabbatar da gaskiya a cikin tsarin kudaden shiga da kuma rashin zuba kudin da aka samu a asusu wanda hukumomin da aka ware mallakin gwamnati ya kamata a ce suna yi, su ne ke ci gaba da fadada matsalar samun kudaden shiga, da haifar da katon gibin kasafin kudi da karin nauyin bashi da kuma wahalhalun da kasar ke fama da su.
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa, gazawar gwamnati na rashin kula tare da yin abin da ya dace a kan hukumomin da ke karkashinta, ya bai wa wasu tsirari daga cikin shugabannin hukumomin fifiko wajen rabon kasafin kudin kasa a kan sauran takwarorinsu.
- Matsin Tattalin Arziki: Yadda Ake Kai Ruwa Rana Tsakanin Masu Gidaje Da ‘Yan Haya
- Tinubu Zai Kai Ziyarar Aiki Netherlands Da Saudiyya
Binciken kasafin kudi a shekarar 2024 na hukumomin gwamnati ya tabbatar da cewa, sama da Naira biliyan 93.429, aka kebe wa hukumomin gwamnati 41; don jin dadinsu tare da walwala a cikin kasafin kudi na wannan shekara, duk kuwa da yadda aka saba rabon kudaden al’umma ga wuraren das am babu su ko kuma ayyukan da babu a cikin kasafin kudin.
Hukumar da ke kula da ala’muran hako danyen mai (NUPRC) ce, ke jagorantar wannan jadawali; inda ita kadai aka kebe mata Naira biliyan 50.4 a matsayin kudaden walwala da jin dadi a cikin wannan kasafi na shekarar 2024.
Abin mamaki, wannan hukuma ta NUPRC kuma za ta kashe Naira biliyan 65.20 a kan ma’aikatanta a cikin wannan shekara, baya ga sauran kudaden da aka kebe mata na rashin gaskiya.
Wacce ke biye da ita kuma ita ce, Hukumar Kula da Ingancincin Abinci da Magunguna ta kasa (NAFDAC), wacce aka ware wa Naira biliyan 6.67 da kuma Kamfanin Inshora na Nijeriya (NDIC). Daga cikin Naira biliyan 21.99 da Kamfanin Inshora na Nijeriya ya ware, don shirin ko-ta-kwana, ya kuma kebe zunzurutun kudi har Naira biliyan 5.3, don jin dadi da walwalar ma’aikatansa kadai a wannan shekara ta 2024.
Kwana-kwanan nan ne, wannan jarida ta bankado yadda Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya, ya kebe wa kansa makudan kudi; kimanin Naira biliyan 920.301, a matsayin kudin kula da ko-ta-kwana, ta hanyar amfani da kyakkyawar dangantaka da Majalisar Dokoki ta kasa, wanda sau tari ake amfani da hakan wajen kara yawan kasafin kudi, don cimma muradu na kashin kai.
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Nijeriya (SON), ita ma an kebe mata Naira biliyan 2.5, don walwala da jin dadin ma’aikatanta, ba tare da bayyana hanyoyin da za bi ta kashe kudaden ba, yayin da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Saman Nijeriya (NCAA), ta fara kashe nata zunzurutun kudaden da suka kai kimanin Naira biliyan 1.164 da aka ware mata a matsayin kudin kula da ko-ta-kwana.
A nata bangaren kuma, Hukumar Kula da Bunkasa Fitar da Kayayyaki Waje ta Nijeriya (NEPZA), ta samu Naira biliyan 1.224 a matsayin kudaden walwala da jin dadin ma’aikatanta, wadanda tuni sun karbi Naira miliyan 978.57 a matsayin kudinsu na alawus.
Har ila yau, hukumomi da kamfanonin gwamnati masu samar da kudade; na fakewa da bin tsarin hukumomin samar da kudaden shiga da aka sahale wa more wani kaso daga cikin kudaden da suke tattarawa, wajen azurta kawunansu da kuma kokarin hana gwamnati da sauran al’ummar Nijeriya samun kudaden da ya kyautu a ce suna samu.
Misali, an kebe musu zunzurutun kudi har Naira biliyan 15,131,971,394.22, a matsayin kudaden alawus-alawus na ma’aikata, da Naira bilyan 10,449,982,489.32 a matsayin kudin ma’aikata na mafi karancin albashi da kuma Naira biliyan 1,806,781,323, don sayen kayan ginin ofishi sakamakon yadda mafi yawan lokuta ake barin kayan gwamnati su lalace, saboda rashin kulawa.
Sai kuma, Hukumar Fansho ta kasa (PenCom), wadda ta shirya kashe Naira biliyan 2.8 a matsayin kudaden kula da ko-ta-kwana, ban da kuma Naira miliyan 342.6 da aka ware, don walwala da jin dadin ma’aikatanta kadai a cikin wannan kunshi na kasafin 2024. Wannan kenan, baya ga sauran wasu kudade da aka dorawa ayar tambaya.
Haka nan kuma, Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), ita ma ta ware Naira biliyan 1.4 a matsayin kudaden kula da ko-ta-kwana a cikin kunshin kasafin kudin na bana.
Haka zalika, Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasa (NASRDA), za ta kashe Naira biliyan 24,704,730,325.78, a wannan shekara ta 2024. Inda aka ware Naira biliyan 16,173,855,919.44 a matsayin jumillar kudin albashin ma’aikatanta da ake kan yin bita na wannan shekara.
Baya ga haka, hukumar za ta kashe Naira miliyan 2,429,660.25, don jin dadi tare da walwalar ma’aikatansu, yayin da kuma Hukumar Kula da Ingancin Sikari (NSDC), ita ma ta samu Naira miliyan 39.6, domin jin dadi da walwalar nata ma’aikatan.
Sauran, sun hada da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa (NIWA), inda ta ware Naira miliyan 367,500,000; sai kuma Hukumar Inshora ta Kasa (NAICOM), Naira miliyan 129.991, Hukumar Kula da Caca ta kasa (NLRC), Naira miliyan 25,419,200; baya ga jimillar Naira miliyan 30,478,850 a matsayin kudin kula da ko-ta-kwana, Hukumar Kula da Kacici-kacicin Kudi Irin na Caca,
ita ma; ta ware Naira miliyan 691,990,785.32 a matsayin kudin kula da ko-ta-kwana kawai, yayin da kuma Ofishin Kula da Ci gaban Harkokin Kimiyya da Fasaha (NOTAP), ya kebe Naira Naira miliyan 8.76 a matsayin kudaden walwala da jin dadi.
Nazarin da muke yi a kan kasafin kudin 2024 na hukumomin gwamnati, ya sake gano yadda Hukumar Kula da Hada-hadar Kasuwancin Man Fetir da Gas ta kasa ta samu Naira miliyan 126.9, yayin kuma da Hukumar Binciken Albarkatun Kasa (RMRDC), za ta kashe Naira miliyan 350, a matsayin kudaden walwala da jin dadin ma’aikatanta, haka nan Hukumar Talabijin ta Nijeriya, ita ma za ta kashe Naira miliyan 73.8 a matsayin kudaden jin dadi da walwala.
Har ila yau, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa (NIS), za ta fitar da Naira miliyan 891,240,537.18, don walwala da jin dadin ma’aikatanta daga cikin asusun kasa; wannan fa baya ga jimillar Naira biliyan 79,860,915,182 da aka ware wa hukumar ce na biyan albashi.
Daga cikin Naira biliyan 1,854,983,014 da ake sa ran za a samu daga Hukumar Kula da Al’amuran Ruwa ta Kasa (NIWMC), za a ware Naira miliyan 10,427,878.75, a matsayin kudin walwala da jin dadi, wanda ba a fayyace yadda za a kashe kunshin kudaden ba.
Haka nan, Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NIMET), ta ware Naira miliyan 925,976,298.50; a matsayin kudaden walwala da jin dadi, inda a dai wannan shekara Hukumar Inshora ta Nijeriya (NSITF), za ta kashe Naira miliyan 100; don walwala da jin dajin ma’aikatanta, bayan jire Naira biliyan 25.63 daga asusun tarayya.
A nata bangaren, Hukumar Inshorar Noma ta Nijeriya (NAIC), za ta kashe Naira miliyan 796.6; a matsayin kudaden kula da ko-ta-kwana daga cikin kudaden da ake sa ran samu Naira biliyan 1.45.
Sannan, Hukumar Kula da Amfani da Sararin Sama ta Nijeriya (NAMA), an ware mata Naira miliyan 200 don jin dadi da walwalar ma’aikatanta, yayin kuma da Kamfanin Dillancin Wutar Lantarki (NBET), zai samu Naira miliyan 385 don jin dadi da walwala daga cikin kudaden da ake sa ran samu kimanin Naira biliyan 463.4 a madadin gwamnati.
Sauran hukumomin sun hada da: Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Naira miliyan 120; Hukumar Tace Fina-finai ta Kasa Naira milyan 10.83, Hukumar Kula da Harkokin Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa (NBC), Naira miliyan N746.4; da kuma Hukumar Kula da Bunkasa Kere-keren Motoci ta Kasa (NADDC), Naira miliyan 491.16, Hukumar Kula da Rajistar Harkokin Kasuwanci (CAC), Naira miliyan 449.87; don jin dadin ma’aikata; sai Bankin Ba Da Bashin Gina Gidaje na Nijeriya (FMBN), Naira miliyan 186.0; Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), Naira miliyan 186.0, sai kuma Kwalejin Horar da Ma’aikata ta Nijeriya (ASCON), Naira miliyan 8.
Haka zalika, an ware wa Hukumar Gudanarwa ta Kasuwar Baje-kolin Jihar Legas Naira miliyan 7.9; Hukumar Kula da Fitar da Rahotannin Kudi ta Nijeriya (FRC); Naira miliyan 105.94, Hukumar Shirya Jarrabarwar Fagen Shiga Jami’a (JAMB), Naira miliyan 950.0, Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Naira miliyan 953.73; Hukumar Kula da Kimiyyar tauraron dan adam ta Nijeriya (NIGCOMSAT), Naira miliyan 6.4; Hukumar Yaki da Satar Fasaha ta Nijeriya, Naira miliyan 45.85; sai kuma Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NEMSA), Naira miliyan 50.
Sauran sun hada da: Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), Naira miliyan 250 da kuma Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Kasa (NEPC), Naira miliyan 3.3.
Da yake tsokaci a kan makudan kudaden da ake kashewa a kan walwala da jin dadin ma’aikatan gwamnati, a daidai lokacin da sauran ‘yan Nijeriya ke cikin mawuyacin hali da fama da gibin kasafin kudi da kuma karuwar basussuka a cikin gida da kuma waje, Shugaban Kamfanin Lancelot; Mista Adebayo Adeleke ya bayyana cewa, irin wannan rabon da aka yi; wata hanya ce ta sake karfafa cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa, “A nawa ganin, duk da mawuyacin halin da tattalin arziki ke ciki; yanzu kuma gwamnati na sake gina wasu hanyoyi na cin hanci da rashawa a hukumance. Idan kuwa bah aka ba, ta yaya za a iya auna fitar da kudade ko tasirin wadannan makudan kudi da sunan ‘kudaden walwala’?
Babban abin mamaki a nan shi ne, duk da wannan ta’asa; har yanzu muna ci gaba da ciwo bashi daga cibiyoyin kasashen waje. Yaya za a yi ku ciyo bashi ku barnatar da kudin?”.
Haka zalika, wani mamba a kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa, kungiyar tasu; ko kadan ba ta gamsu da wadannan alkaluma na kasafin kudi ba.
Sannan kuma, ya yi kira da a tabbatar da cewa; an bi diddigin wadannan ma’aikatu da hukumomi, wadanda aka yi wa lakabi da kudaden walwala da jin dadi, don samun cikakken bayani.
“Muna sa ran gwamnati da sauran hukumomi za su fitar da nasu kason na walwala da jin dadi. Hasali ma, da kudade masu yawa da kadan; ba za mu iya yin tsokaci a kansu ba, tun da ba a fayyace yadda za a batar da su ba. Muna sane da cewa, wasu mutane da sunan walwalar ma’aikata; suna karkatar da ire-iren wadannan makudan kudade zuwa cikin aljihunsu tare da cutar da ma’aikatan Nijeriya.”
“Ana fakewa da Ma’aikatan Nijeriya ne kawai, amma wasu ‘yan kalilan mutane ne ke amfani da sunansu da ma’aikatu da kuma sauran hukumomi, suna karkatar da kudaden da aka tanadar musu,” a cewar tasa.