Duk da kashe sama da naira biliyan 200 wajen gudanar da shirye-shiryen kidayar jama’a da gidaje tun daga shekarar 2014, gwamnatin tarayya ta yi gum kan gudanar da kidayan da aka dage.
An fara gudanar da shirye-shiryen kidayar jama’a ne tun a farkon wannan shekara, wanda aka saka ranar 3 ga Mayun 2023, amma sai tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta dage kidayar har sai wani lokaci.
- Shin Wasan Kwaikwayon Na Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Kawo Karshe Ne?
- Gwamnati Ta Samo Jarin Fiye Da Dala Biliyan 2 A Bangaren Wutar Lantarki
A cewar hukumar kidaya ta kasa (NPC), babban makasudin daukar matakin dage aikin kidayar jama’a a shekarar 2023 shi ne, bayar da dama ga gwamnati mai zuwa.
Ta ce akwai bukatar sabuwar gwamnati ta kasance mai cikakken bayani kan tsarin da ake amfani da shi wajen tattara bayanan kidayar jama’a.
Amma, bayan watanni biyar da kafa sabuwar gwamnati, ba a ji komai ba game da gudanar da lamarin kidayar.
Nijeriya dai na daya daga cikin kasashen yammacin Afirka da ba a san hakikanin yawan mutanenta ba, sannan kuma ta dogara ne da alkaluman kididdigarta a kan hasashe.
An dai gudanar da kidayar jama’a da jidage ta karshe ne a shekarar 2006, kuma tun da ana gudanar da kidayan a duk bayan shekaru goma, ya kamata Nijeriya ta yi kidayar jama’arta na gaba a shekarar 2016, amma sakamakon siyasa da lamari da kudade hakan bai yuwu ba.
Lokacin da aka tuntubi daraktan hulda da jama’a na NPC, Dakta Isiaka Yahaya, ya ce har yanzu hukumar na jiran sanarwar Shugaba Kasa Ahmed Tinubu kan gudanar da kidayan.
“Mun gana da shugaban kasa tare da gabatar masa da tsayinmu, har yanzu muna jiran mu ji ta bakinsa,” in ji shi.
Ya ce jaddada cewa tabbas akwai yuwuwar gudanar da sahihin kidaya a Nijeriya.
Sakamakon rashin gudanar da kidaya ya sa an kasa samun cikakkun bayanai dalla-dalla kan yawan al’ummar kasar da rashin samun tanadin zamantakewa da na ci gaban tattalin arziki, wadanda ke kawo cikas wajen aiwatar da manufofi a Nijeriya.