Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa kuma Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Henry Seriake Dickson, ya ce duk da kasancewarsa ɗan adawa a jam’iyyar PDP, tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari, ya hana a murɗe masa zaɓe.
Sanata Dickson ya ce babu wani zaɓe da ya fi nasa zafi a lokacin da ya tsaya takarar neman wa’adin mulki na biyu a 2015, amma Buhari ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa ta APC ba ta yi masa maguɗi ba.
- Yadda Hadarin Mutuwa Ke Karuwa Yayin Ko Bayan Saduwa Da Iyali
- An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Ya bayyana hakan ne a wajen zama na musamman da Majalisar Dattawa ta yi don tunawa da rayuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A cewarsa: “Da kansa Buhari ya kira ni a 2015, ya ce ya faɗa wa shugabannin INEC, sojoji da DSS cewa su faɗa wa jami’ansu su bi doka su bar mutane su zaɓi wanda suke so.”
“Ya ce an taɓa yi masa maguɗi a baya, kuma yanzu ne shugaba ba zai bari a yi wa wani ba. Ya kuma ce na tafi na fara yaƙin neman zaɓe.”
Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari.
Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu bai cancanta ba, amma Buhari bai matsa lamba kan kotun ta sauya hukuncin ba.
“A lokacin mutane sun shirya rantsar da ɗan takarar APC a Bayelsa, amma cikin ƙasa da awa guda, kotun ƙoli ta soke nasararsa. Duk da haka Buhari ya karɓi hukuncin,” in ji shi.
Ya ce Buhari shugaba ne na gari, wanda duk da bambancin siyasa da ra’ayi, bai taɓa nuna bambanci tsakanin gwamnoni ba, ko suna APC ne ko na jam’iyyar adawa, yana girmama su tare da ba su tallafi iri ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp