Katafariyar Matatar Mai ta Dangote, ta kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da suka dauki hankali tare da tayar da kura a Nijeriya; tun daga kimanin Makoni uku da suka gabata yayin da mahukuntan matatar suka fara korafin cewa kamfanonin kasashen waje da ke hako mai a Nijeriya na yi musu zagon kasa wajen samun danyen man da za su rika tacewa.
Al’amarin ya yi tsamari a makon jiya, sakamakon zargin da daya daga cikin shugabannin hukumomi masu kula da al’amuran mai ya yi na cewa, matatar man ta Dangote; na son yin babakere a harkar man fetur a Nijeriya tare kuma da zargin cewa, man da take samarwa; bai kai ingancin da ake bukata ba ko a Afirka ballantana a kasashen duniya da suka ci gaba.
- Kyari Ya Musanta Zargin Dangote Na Wasu Ma’aikatan NNPC Na Hada-hadar Mai A Malta
- Barazana Ga Matatar Dangote: Kwankwaso Ya Bukaci Kare Muhimman Kadarorin Kasa
A tattaunawarsa da manema labarai na fadar shugaban kasa a makon da ya gabata, Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da kuma Sufurin Man a Nijeriya (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed; ya musanta zargin da wasu ‘yan kasar ke yi na cewa, ana kokarin durkusar da matatar man ta Dangote.
Har ila yau, wasu daga cikin abubuwan da shugaban ya bayyana a matsayin zarge-zarge; sun hada da cewa, ba gaskiya ba ne cewa; ana wa matatar kafar ungulu don hana ta samun nasara.
A wani bangare na gugar zanar da ya yi, Injiniya Ahmed ya ce, har yanzu ba a kammala aikin gina matatar man Dangoten da ke Lekki a Jihar Legas ba; inda aikin da ake yi bai wuce kashi 45 cikin 100 ba, sannan ya bayyana cewa; har zuwa yanzu ba a bai wa matatar lasisin fara aiki ba.
Sai dai kuma, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote; ya mayar da martani mai gauni a kan kalaman Shugaban Hukumar ta Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da kuma Sufurin Mai a Nijeriya (NMDPRA).
Ya mayar da martanin, yayin ziyarar da wasu ‘yan majalisar wakilan Nijeriya; suka kai matatar ciki har da shugaban majalisar, Hon Abbas Tajuddeen da mataimakinsa Hon Kalu.
Da farko, Dangote ya bayyana wa ‘yan majalisar da ma sauran ‘Yan Nijeriya cewa, idan ba a yaba musu ba ai ba a kushe su ba, domin su kadai suka yi hobbasar gina matatar mai karfin tace gangar mai 650,000 a kullum ba tare da samun wani tallafi daga gwamnati ba. “E, lallai gwamnatin Legas ta yi mana sauki amma babu wani abu kyauta da aka yi mana, ko filin da aka ba mu muka gina matatar sai da muka biya Dala Miliyan 100… Haka nan hannun jarin da NNPC ya ce zai zuba da kashi 20 cikin 100 bai yiwu ba, mun kara musu lokaci bisa yarjejeniyar da muka yi har zuwa karshen watan Yunin da ya wuce amma babu labari, daga bisani suka ce sun sauya shawara, yanzu kashi 7 kawai za su saka hannun jarinsu.” In ji shi.
Dangote ya kuma kara tabbatar da sahihancin man da suke tacewa na dizel “domin wadanda suka saya sun sake dawowa suna so daga sassa daban-daban na duniya. Zuwa yanzu matatarmu ta fitar da manta zuwa wasu kasashen Tarayyar Turai da Singapore da Lome.
Dangote ya yi mamakin dalilin da ya sa wata hukuma ta daidaita al’amura kamar (NMDPRA) da ya kamata ta kare masana’antun cikin gida amma kuma ta koma tana hantararsu har ma da yin karya a kafofin watsa labarai don tabbatar da bukatar ci gaba da shigo da gurbataccen man fetur a cikin kasa.
“Ina kira gare ku (majalisa) da ku kafa kwamitin da zai dauki samfura a gidajen mai, mu dauki namu samfurin, domin dole ne in gaya muku cewa duk takardun tantance sahihancin mai da mutane ke yawo da su na bogi ne. Ina dakunan gwaje-gwajen da aka gudanar da binciken? Ta yin haka, za ku iya gaya wa ’yan Nijeriya ainihin gaskiyar da suka cancanci su sani. Kushe kasuwancin wani kamfani daga hukumar daidaita al’amura da ta kamata ta kare kamfanin abin bakin ciki ne da takaici
“Ba mu san cewa za ku nemi mu tsaya a kan hanya mu dauki samfurori daga wasu gidajen mai ba. Ban san abin da kuke so ku yi ba sai da muka zo nan kuma kuka nemi gwaji. Wani abu mafi dacewa ma shi ne membobinku ne suka tafi kai-tsaye suka dauki samfuranmu kuma na tabbata kun yi mamakin sakamakon da kuka gani. Bisa sakamakon, za ku ga muna samar da dizal mafi inganci a Nijeriya.”
Dangote ya fito karara ya kalubalanci hukumar (NMDPRA) da ta bayyana ingancin man da ake shigo da su daga kasashen waje, yayin da ya yi kira da a tantance ba tare da nuna son kai ba domin sanin abin da zai dace da muradun ‘Yan Nijeriya. “Muna samar da dizal mafi kyau a Nijeriya. Abin takaici ne a ce maimakon a kare kasuwancinmu, amma mai ba da kulawa kuma yana yi masa zagon kasa. Kofofinmu a bude suke ga hukumar don gudanar da gwaje-gwaje a kan samfuranmu a kowane lokaci; gano gaskiyar lamari tare da bayyana wa jama’a ne mafi muhimmanci a gare mu. Zai yi kyau ita hukumar (NMDPRA) ta nuna dakin gwaje-gwajenta ga duniya domin ‘yan Nijeriya su rabe tsaki da tsakuwa. Babban abin da muke fatan gani shi ne Nijeriya ta bunkasa, saboda muna da karancin ci gaba.
“Shugaban majalisa da sauran membobi, kun ga sakamakon gwajin sahihancin man da aka yi. Na yaba da wannan hikima taku wajen zuwa gidajen mai ku dauki samfurin main a matatarmu. Namu ya nuna akwai sinadarin sulfo ppm 87.6, akalla dai 88, yayin da na wasu kuma ya haura ppm 1,800. Duk da cewa Hukumar NMDPRA ta amince wa matatun main a gida su samar da mai da zai kunshi sidarin sulfo 650 har zuwa Janairun 2025, kamar yadda ECOWAS ta amince, namu bai kai haka ba, zuwa mako mai zuwa, mun sha damarar samar da man da yake kunshe da sulfo ppm 10 kawai, domin ya yi daidai da ingancin da ake bukata a Tarayyar Turai. An tsara cewa man da za a shigo da shi ka rya zarce ppm 50, amma kamar yadda kuka gani daga wasu gidajen mai, da ‘yan kasuwa suka shigo da shi, ya gaza samun sahihancin da ake bukata.” In ji Dangote.
Ya bukaci a rika zuwa gidajen mai kai-tsaye ana daukar samfuran man da ake son tantance sahihancinsa domin a nan ne za a samu asalin man da ake shigo da shi, yana mai cewar, “na yi ammanar Farouk Ahmed ya yi magana ne ba tare sanin yadda matatarmu take ba. Mun yi nasarar fitar da dizal da man jirgi zuwa Turai da yankin Asiya kuma ba mu samu wasu korafe-korafe ba. A hakika ma, wadanda suka saya sun sake dawowa suna son kara sayen man namu,” ya bayyana.
Sakamakon wannan kurar da ta taso dai, Alhaji Aliko Dangote ya ce hukumar gudanarwar kamfanoninsa ta dakatar da shirin da take yi na kafa masana’antar sarrafa karafa da take yi, “domin idan muka ce za mu yi, za a rika kiranmu da sunaye na batanci… Akwai sauran ‘Yan Nijeriya da suke da kudi fiye da mu ma, su je kasashen waje (da suka jibge kudadensu) irin su Dubai, su kwaso kudaden su zo su kafa masana’antu a Nijeriya.” Kamar yadda ya nunar.
Ko shakka babu, wannan tataburza a tsakanin bangarorin biyu; ta yi matukar tayar da kura tare da jan hankalin ‘yan Nijeriya, musamman masana tattalin arziki da sauran masu yin fashin baki a kan harkokin yau da kullum.
Fitaccen mai yin fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Adamu Abubakar ya danganta kalaman da aka yi a kan matatar man ta Dangote a matsayin na batanci wanda ya ce zai shafi makomar ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma ita kanta Nahiyar Afirka.
A cikin wata sanarwa, da Adamu ya raba wa manema labarai ya ce, furucin da aka yi a kan matatar wani yunkuri ne kawai na salon yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, wanda kuma ya yi daidai da cin amanar kasa.
Har ila yau, ya kara da cewa; ga ‘yan kasuwa masu tasowa a Nijeriya da kuma wadanda ke yankunan Afirka, wannan matatar mai ta Dangote, tamkar madubi ne da zai haskaka musu hanya tare da kara musu karsashi, wajen cimma nasara a harkokin kasuwancinsu.
“tamkar wani yunkuri ne na son yi wa dimbin ‘yan Nijeriya kafar ungulu, musamman idan aka yi la’akari da dimbin matasan da za su samu aikin yi a wannan matatar man fetur ta Dangote.
“Matatar man ta Dangote, masana’anta ce wadda za ta sama wa ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan Afirka alkibla mai dorewa tare kuma da samar musu ci gaba ta bangarori daban-daban.” In ji shi.
Haka zalika, Malam Abubakar Aliyu; shi ma ya kalli al’amarin a matsayin wata babbar barazana, musamman ga masu zuba jari a Nijeriya, domin kuwa a cewarsa; akwai alamun da ke nuna ana yi wa masu zuba hannun jari zagon kasa, domin abin da ake yi wa Dangote; zai tsoratar da masu zuba hannun jari na cikin gida da kuma na wajen kasar.
Aliyu ya kara da cewa, babu shakka hakan na iya yin matukar illa ga tattalin arzikin saboda idan har ba a zuba hannun jari ba; dole ne ya kasance ana fitar da kudaden kasar waje, domin sayo kayayyakin da za a yi amfani da su.
Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin a wani shiri na Gidan Talabijin na Channels, fitacen lauyan nan na kare hakkin Dan’adam, Femi Falana SAN, ya bayyana cewa Lallai ai abin da gwamnati take yi na hantarar matatar man Dangote tamkar caka wa kanta wuka ne.
Ya bayyana cewa, ta yaya gwamnati za ta garzaya kasashen waje ta ce tana neman masu zuba jari amma kuma tana kyarar masu zuba jari na cikin gida? A ina ake haka a duniya? Gwamnati ta saki layi ainun. Tun farko da ta ce man dizel na Dangote ba shi da inganci to me ta yi a kai? Ta bari ai an ci gaba da sayarwa a Nijeriya. Kuma yanzu Dangote ya kalubalance su, su zo da sahihin gwaji a tsakanin mansa da wanda ake shigowa da shi. Gaskiya wannan abin kunya ne. Gwamnati ta koma ta sake tunani.
Ya kara da cewa, Nijeriya ce kadai a cikin manyan kasashe masu arzikin mai na duniya da take shigo da tataccen mai daga kasashen waje, an kashe makudan kudade amma har yanzu matatun mai na kasar ba su aiki. Abin kunya ne wannan.
Hakazalika, a cewarsa, zancen da ake yi na ya kamata NNPC ya mallaki kashi 20 na hannun jari a matatar man Dangote ai ina ga muna bukatar fiye da hakan, domin matatar za ta taimaka wajen samun wadataccen mai a Nijeriya wanda al’ummar kasa za su samu sauki na walhalun da ake sha a kan man.
Bayan wannan dambarwa ta yi kamari ne kuma, sai gwamnatin tarayya ta fara yunkurin sasanci a tsakanin bangarorin biyu, inda Karamin Ministan Man Fetur; Heineken Lokpobiri, ya jagoranci wani zama tsakanin Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL), Mele Kyari da Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da kuma Sufurin Mai a Nijeriya (NMDPRA), Farouk Ahmed da Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da kuma Shugaban Hukumar Kula da Al’amuran Danyen Mai ta Kasa (NUPRC), Gbenga Komolafe, a ranar Litinin da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da Ministan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya bayyana cewa; ganawar wani yunkuri ne na kokarin magance matsalolin da matatar man fetur din ke fuskanta.
Ministan ya kara da cewa, dukkanin bangarorin sun lashi takobin lalubo bakin zaren tare kuma da nuna jin dadinsu da wannan yunkuri na sasantawa da ake kokarin yi a tsakaninsu.
Tun bayan zargin matatar man fetur ta Dangoten da hukumomin ke yi, na fitar da man dizel mara inganci; wanda kuma ta musanta ta hanyar gudanar da gwaji a gaban wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayya a ranar Asabar da ta gabata, wannan ne karo na farko da bangaren gwamnatin tarayya ta magantu, kan wannan dambarwa.
Sai dai kuma, ga dukkan alamu tsugune ba ta kare ba, domin kuwa bayan zaman wannan sasantawa ne; Shugaban Rukunin Kamfanonin Mai na NNPCL, Mele Kyari ya sake mayar wa da Aliko Dangote martani; ta hanyar musanta ikirarin da ya yi na cewa, wasu daga cikin ma’aikatan NNPCL na gudanar da hada-hadar matatar mai a Malta.
Alhaji Aliko, wanda ya yi wannan ikirari a yayin ganawar da ya yi da ‘yan majalisar tarayya ya bayyana cewa; wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin na NNPCL da kuma wasu daga cikin dillalan man fetur, na da masana’antar hada-hadar man a yankin tsibirin Bahar Rum.
Shugaban na NNPCL, Mele Kyari ya musanta hakan ne a shafinsa na D (Twitter), inda ya bayyana cewa, shi da sauran ma’aikatansa, babu wanda ya mallaki wani kamfani da yake gudanar da hada-hadar mai da ake zargi.
Har ila yau, ya nanata kudirin kamfanin na NNPCL, wajen bin bin doka da kuma oda. Sannan, ya bayyana kudirinsa na cewa; duk wani ma’aikacinsa da aka samu yana da hannu a irin wadannan ayyuka na hada-hadar mai, ko shakka babu zai fuskanci hukunci tare kuma da mika shi hannun hukuma; domin hukunta shi.
Idan ba a manta ba, Dangote ya koka kan yadda kamfanonin waje ke kin sayar wa da matatarsa danyen mai, domin fara tacewa da sayarwa a cikin gida Nijeriya.
Sakamakon wannan rikici dai, rahotanni, sun tabbatar da cewa; a halin yanzu Dangote ya karkata akalarsa wajen sayo danyen man daga kasashen Libiya da Angola, domin tace man fetur da za su fara fitarwa kasuwa a watan Agustan wannan shekara da muke ciki.
Duk da haka, ya sha alwashin ci gaba da gwagwarmaya kamar yadda ya saba, “kusan duk tsawon rayuwata gwagwarmaya nake yi. Na yi Imani da Allah, don haka babu wanda nake jin tsoro, zan ci gaba da gwabzawa,” in ji Dangote a wani faifan bidiyo.