Miliyoyin yan Nijeriya sun kagara da ganin lokacin da manyan zabuka za su gudana salim-alim ba tare da tashe-tashen hankula irin na kare-jini biri-jini ba, al’amarin da kusan kowane lokaci yake jawo asarar rayuwa, raunata jama’a tare da asarar dimbin dukiya ta miliyoyin naira; rikicin da kan barge tun kafin zaben, a sa’ilin da yake gudana da ma bayan kammala shi.
Wannan rikicin a lokutan manyan zabukan, ya zama alakakai ga dimukuradiyyar Nijeriya, wanda ake zargin yan siyasa da hannu dumu-dumu wajen kitsa shi, musamman kusan dukan manazarta sun yi ittifakin cewa su ne kanwa uwar gami saboda a zahiri su ne suka cin gajiyar sa. Saboda babu yadda za a yi mai cikakken goyon bayan jama’a ya tayar da hayaniya.
Yan siyasa sun yi kaurin suna wajen zargin su da amfani da matasa a harkokin dabar siyasa ta hanyar basu miyagun kwayoyi don tayar da zaune tsaye tun a lokutan yakin neman zabe, a lokacin zaben kansa da ma bayan kammala shi a daidai lokacin da suka hango rashin nasara. Wadannan maras kishin al’umma suna da tunanin dole sai sun ci zaben ko ta tsiya ko ta tsiya-tsiya, wanda a nan ne gizo ke sakar.
Hakanan ma, babban abin da miliyoyin yan Nijeriya ke son sani shi ne, shin ina yarjejeniyar da kungiyoyi masu rajin kare tsarin dimukuradiyya kan shiryawa yan siyasa tare da sanya hannu cewa sun yi alkawarin zabukan zasu gudana lafiya? Ko kawai taron yaudara ne wanda bai wuce na shan shayi a teburin mai shayi ba? Saboda idan ba haka ba, ta yaya ana magani kai yana kumbura; babu wani ci gaban da kulla wannan yarjejeniya ya kawo a tsarin dimukuradiyya a Nijeriya.
Sannan shin dole ne sai ta hanyar rikici da tashin hankali ne ake cin zabe; ko kuma tashin hankali a lokutan zaben yana daya daga cikin sharuddan dimukuradiyya? Saboda gaskiya yan Nijeriya suna son yan siyasa da masu rajin kare tsarin a Nijeriya su amsa wadannan tambayoyin, ko kuma a dakatar da wannan rikicin haka nan! Domin ko ba komai, masu hikima sun ce: zaman lafiya yafi zama dan Sarki.
Rahoton da Rundunar Yan-sandan Nijeriya ta fitar, kan tashe-tashen hankulan da aka samu a lokutan zaben 2023, na shugaban kasa da yan majalisun tarayya tare da na gwamnoni da na yan majalisun dokoki, wadanda suka gudana a cikin watannin Fabarairu da Maris na 2023, sun gano an aikata laifuka 489 a lokacin zaben tare da kama kimanin mutum 781 da ake zargi da tayar da rikicin.
Sanarwar ta fito ne daga bakin Babban Sifeto Janar na Yan-sandan Nijeriya, IGP Usman Baba, a lokacin da ya gudanar da taro na musamman da manyan jami’an Yan-sanda a birnin Tarayya dake Abuja a ranar Litinin da ta gabata.
IGP Baba ya kara da cewa, “A cikin jihohi 36 dake fadin kasar nan tare da Abuja, mun samu jimlar aikata manyan laifuka 489 tare da nasarar kama kimanin masu laifuka 781 a lokacin zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya, zaben gwamnoni da yan majalisun dokoki, tare da tarin makamai daban-daban 66.”
“A takaice jimlar manyan laifukan da muka samu a lokacin zaben shugaban kasa 185 ne tare da kama mutum 203 da makamai 18. Sai adadin manyan laifukan da muka gano su ne 304 a lokacin zaben gwamnonin tare da damke mutum 578 tare da makamai 48.”
A nata bangaren Hukumar SERAP (Socio-Economic Rights and Accountability Project) ta bukaci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gaggauta kafa kwamiti mai zaman kansa wanda zai gudanar da binciken kwakwaf dangane da zarge-zargen rikici a lokacin zabe tare da cin hanci da rashawa wanda ake yiwa gwamnoni da mataimakan su a zabukan da aka gudanar bada dazena ba.
SERAP ta kara da cewa, “Cikin hanzari, ba tare da bata lokaci ba, ka binciki zargin laifukan da aka tafka na yiwa dokokin zabe hawan kawara, tare da sauran laifukan da aka aikata a lokutan manyan zabukan, a nemo wadanda suka aikata laifukan da wadanda suka dauki nauyin su, kuma ka tabbata an kama su da gurfanar dasu a gaban kotu, komai girma da matsayin su a siyasa ko yan garancinsa.”
Wadannan suna kunshe a cikin wasikar da Mataimakin Daraktan Hukumar SERAP, Mista Kolawole Oluwadare ya aikewa hukumar INEC ranar 25 ga watan Maris, 2023 inda ya kada baki ya ce: “Sakamakon wadannan zarge-zargen aikata hargitsin zabe da sauran manyan laifuka a lokacin zaben, abin ayi Allah wadarai ne, sannan ya kamata a cukumo wadanda suka aikata laifukan tare da masu daukar nauyinsu, wanda a zahiri hakan yiwa kudin tsarin mulki karan tsaye ne, kuma ya saba da dokokin zabe na kasa da kasa.”
SERAP ta kara da cewa, “A sashe na 52 na ICPC, ya bai wa INEC ta nada kwamitin da zai gudanar da binciken kwakwaf dangane da zarge-zargen tayar da rikici a lokacin zabe tare da sauran laifukan da aka aikata a lokacin zabe wadanda suka hada da cin hanci da rashawa, a kowane Gwamnonin jihohi da Mataimakansu.”
“Ku tabbatar ko su waye, ku bincike su da bayyana sunayen su, a matsayin masu hannu dumu-dumu wajen tayar da rikicin zabe da sauran laifukan da suka aikata a lokacin zaben 2023, ku tura wa yan siyasar zazzafan martani hadi da magoya bayan su, ku nuna musu ba zai yuwu ayi rotsi a kwana sake ba; bayan sun cutar da yan Nijeriya.”
Wanda ko shakka babu, idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, wasu yan siyasa su yi abin da suka ga dama da sunan neman mulki ko ta halin kaka, ba zai haifarwa kasarmu da mai ido ba. Saboda haka ya dace hukumomin da abin ya shafa su yi duk abin da ya kamata wajen dakile ta’addanci da tayar da zaune tsaye a layukan zabe da sauran su. Bai kamata mai dokar bacci ya rakabe da ‘gyangyadi ba’.
Dauki misali da abin da ya faru a jihar Kano, inda rahotanni suka nuna yadda wani dan siyasa ya yi amfani da makami wajen kashe mutane tare da raunata wasu, babu gaira babu dan dslili. Sannan kuma aka barshi, shikenan ya kashe maras galihu, ya ci banza? Har wala yau, irin wannan ya faru a jihohi da dama a kasar nan, kuma bisa ga dukkan alamu babu wasu kwararan matakan da za a dsuka kan masu laifukan, saboda kasancewar su shafaffu da mai!