Wakiliyarmu Amina Bello Hamza ta tattauna da Ramatu Bello matashiyar da ta yi karatun boko har zuwa matakin digiri na biyu (Master) amma hakan bai sa ta yi watsi da sana’a ba. Ga dai yadda hirar ta kasance.
Da Farko Za Mu So Ki Bayyana Mana Sunanki?
Suna na Ramatu Bello, ina zaune a garin Samarun Zariya a Jihar Kaduna, na yi karatu na tun daga Firamari, Sakandari, Difloma, Digiri zuwa matakin Masters duk a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ko Malamar na da aure?
Lallai ina aurena
Wanne sana’a kike yi a halin yanzu?
Sana’ar da nake yi a halin yanzu sshi ne sayar da duk wani nau ‘i na kayan kitchen kamar su Fridge, Tukunya, Cooler da set din robobi, a takaice dai muna hada kayan dakin amarya.
Menene ya baki sha’awar fara wannan sana’ar?
Tunda na taso a gidan mu naga mahaifiya ta na sana’a sai ya zama nima ina da wannan burin na ganin na yi saye da sayarwa nima, sai na yi wa mahaifata magana ta kuma bani shawarar yadda zan gudanar da nawa sana’ar.
Sannan ina da burin na samar wa kaina aikin yi ba sai mutum ya jira an yi masa wani abin ba, zai iya taimaka wa kansa da iyayensa da kuma abokan arziki.
Idan Mutum Na Son Fara Wannan Sana’ar Wani Abu Zai Tanada Don Samun Cikakkiyar Nasara?
Idan zaka fara wannan sana’ar kana bukatar ka sayi kayan ko ba yawa ta yadda idan mutum ya tambaya zaka iya nuna masa sai ya tabbatar da lallai kana sayar da kayan. Sannan yadda zamani ya zo na ‘ social media’ zaka iya anfani da wayar ka domin daukan hotan kayan ka nuna wa masu saya da kuma yada kalolin kayan da za a iya samu a wajen ka da kuma yadda za a sami kayan cikin sauki.
Tayaya Kike Tallata Hajojinki?
Ni gaskiya nafi sayar da kayana a cikin ‘yanuwa da abokan arziki, idan mutum ya zo ya saya kaya na sai kiga gobe ya kawo wani shima wannan da ya zo saya shima zai kawo wani. Sai kuma da zamani ya zo Ina anfani da Facebook (Rahama Bello Hamza) ko a kira number ta 07063527841 ko su yi min magana ta Whatsapp.
Ko Zaki Bayyana Mana Wani Abun Da Ya Taba Faruwa Da Ke Na Farin Ciki Ko Akasin Haka A Rayuwarki Na Wannan Sana’ar?
Alhamdulillah, kullum muna cikin farin ciki don gaskiya ba ranar da za mu tashi ba a nema kaya a wajen mu ba, amma akwai kayan dakin da na hada abun ya yi min dadi sosai bawai don nawa yafi na kowa ba amma ban yi tsammani ba abin ya zo gareni ya sa har yau na kasa mantawa. Na bakin ciki kuma akwai shi amma farin cikin yakan danne shi.
Wanne Shawara Kike Da Shi Ga al’umma?
Shawara na shi ne lallai yanzu rayuwa ta yi tsada amma ba abin da ya kai hakuri dadi, idan muka yi hakuri da duk wani manyan burikanmu sai mu ji dadin yin rayuwa, mu dai na kallon na sama damu a kullum mu kalli na kasa damu sai mu ji dadin rayuwa. Sannan duk wanda yake da damar yin karatu ya yi iyakan kokarinsa na ganin ya cimma nasara, sannan ya kuma hada da sana’a domin dogaro da kansa. Yin hakan kuma ba zai yuwuba sai an yi hakuri so sai a kan duk abin da za a fuskanta.
Ya Kike Ganin Yanayin Tarbiya A Wannan Lokacin?
Tarbiya a zamanin nan gaskiya ba a magana sai dai Allah ya tausaya mana. Saboda mafiya yawan iyaye su kan gaza wajen sauke nauyin da ya hau kan su na kulla da ‘ya’yan su.
A kula da karatunsu idan babu halin karatu a samu a koya masu sana’a domin rashin abin yi shi ne ke haifar da tabarbarewar tarbiya, idan baka ba wa yaro aikin yi ba shi zai ba wa kansa. Sannan idan yaro ya zama ba abun yi zai sa zuciyarsa ta gurbace har ta kai shi ga aikata abin da ba a so.
Menene Burinki A Wannan Sana’ar?
Babban burina a wannan sana’ar shi ne naga na bude nawa babban shagon inda zan zuba ma’aikata, ta yadda za su dinga samu a kasa na, suma su samu su dogara da kansu.