ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

by Rabi'at Sidi Bala
18 seconds ago
Kannywood

Shafi ne daya saba zakulo muku fitattun Jaruman finafinan hausa manya da kanana, dake cikin masana’antar shirya finafinan hausa ta Kannywood. A yau ma shafin na tafe da wata matashiyar jarumar daga cikin jarumai masu tasowa wato, HAUWA SANI KUJAMA wacce aka fi sani da HAUWA KUJAMA. Inda ta bayyanawa masu karatu irin kalubalen da ta fuskanta kafin ta fara fim, har ma da wasu batutuwan da suka shafi rayuwarta.

Ga dai tattaunawar tare da wakiliyar jaridar LEADERSHIP HAUSA RABI’AT SIDI BALA Kamar haka;

  • BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani
  • Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da sunan da aka fi saninki da shi.

ADVERTISEMENT

Da farko dai sunana Hauwa Sani, wacce aka fi sani da Hauwa Kujama.

Ko za ki fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinki?

LABARAI MASU NASABA

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

An haife ni a garin Kano, karamar hukumar Nasarawa, Giginyu, Mahaifana ‘yan Sakkwato ne. Na yi aure a Kano ina da yara na guda uku, namiji daya mata guda biyu. Na yi firamare da Sakandare, a garin Kano.

Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma harkar fim?

A baya ban taba jin zan yi fim ba dan bana ra’ayi, ban taba jin abun yana burgeni ba, ban kuma taba sa shi a raina ba har in ce zan yi ba. Amma sakamakon ina tare da ‘yan fim din ina dan harkar turarurruka, kayayyaki, ‘yan dai abubuwa ina dan kai musu, har na shaku dasu, na ga yadda suke yi. Har wata rana bana mantawa ana ‘shooting’ din wani fim, sai na kora wata da nake kai mata turarurruka, sai na ce mata “Maryam kina ina?” Tace min tana ‘location’, na ce mata “yau dai ki kwatanta min inda ake yi” to, da na je na gani abin dai ya burge ni, sai na fara jin ni ma a raina ina so. Sai wani yaro yana ‘comedy’ ya rasu Kamal Aboki Allah ya ji kansa da gafara, kanina ne dan unguwar mu daya ga gidanmu ga gidansu kani ne a gu na. Sai na ce kai nima yau ‘comedy’ din nan dai ayi da ni, sai aka yi da ni. Kuma tun daga lokacin abin ya shiga raina har aka kira ni aikin kwana casa’in, shi na fara yi. Mamana da babana sun rasu sai Antina ta ce ba ta yarda nayi ba ni kuma ina so. Akwai lokacin da na ce mata na je unguwa ni kuma an fara aikin kwana casa’in wajen na je, bayan na je sai na ga ai mahaifiyata ce bai kamata na yi mata karya ba sai na koma na same ta na ce, “ba unguwa zan je ba kin ga kwanaki na je na yi aikin kwana casa’in kin yi min fada” to, yanzu sun kuma kira na ne”. Sai ta ce a’a sai dai na yi mata alkawari zan kare mutunci na, kuma na yi alkawari na ji a raina da mahaifiyata nake wannan alkawarin. Sai na zauna nayi mata rantsuwa na ce in Allah ya yarda ina kuka na ce, “in Allah ya yarda ni dai wannan layin a cikin jikina sana’a na dauke shi. Kuma in sha Allahu ba zan ci amanarta ba a wannan tafiyar dai ta aiki, ba zan ce na tafi aiki na tafi wani guri na daban ba, na yi mata alkawari zan kare mutunci na. Kuma ta ce ta amince Allah ya bayar da sa’a, dan duk sanda zan fita ma sai ta yi min addu’a.

Ya gwagwarmayar farawar ta kasance?

‘Yan’uwana da ‘yan’uwan babanmu da suka fara gani yadda ki ka san na cike fom na ‘yan ‘kidnapping’ abun haka ya kasance min, aka rika kira na ba su yarda da hakan ba, to ni kuma na riga na san yayata uwa daya uba daya ita ce babbar yayarmu ita ce komai nawa jigona, duk duniya na riga na san ta amince min. Ita ce wacce ta san ci na, sha na, sutura ta, har ma ta kula da ‘ya’yana tunda ta amince min, kuma ita ce ta san damuwata sai na ga babu wanda ya isa ya ce zai hana ni. Da dai suka gama abinsu kuma har suka zo na fahimtar da su na ce ni fa wannan abun sana’a na dauke shi, sai kuma suka fahimta su da kansu ma suna yi min addu’a. Dan har so suke ma su gafim din da nake ciki ma su yi farinciki su yi murna.

Ya farkon fara fim dinki ya kasance?

Farkon farawar da ya kasance, yadda ki ka san tsowurar jaruma zan ce miki, farko dai abun gabana yana faduwa ko da aka saka min kyamara jikina yana rawa dai sai na daure, sai na yi musu abin da suke so ba a samu matsala ba. Dan su ma suka rika mamaki suka ce min na taba yi ne? na ce masu a’a.

Da su wa ki ka fara haduwa farkon shigarki masana’antar kannywood?

Bayan na yi aikin kwana casa’in, sai aka kira ni aikin Izzar So, na fara haduwa da su Lawan Ahmad da sauran jarumai da suke cikin Izzar So.

Daga lokacin da ki ka fara fim zuwa yanzu, kin yi finafinai sun kai kamar guda nawa?

Gaskiya na yi su da dama ba zan iya fado adadinsu ba, amma kadan daga cikinsu akwai; Izzar So, Sirrin Boye, Dadin Kowa, Manyan Mata, da dai sauransu.

Wane fim ne ya zamo bakandamiyarki cikin finafinan da ki ka fito ciki?

Akwai Izzar So, akwai Laure. Shi Laure ba wani yi nayi da yawa ba, amma yadda ki ka san da shi na fara, saboda duk inda na shiga ma ce min ake yi Lauren.

Wane irin nasarori ki ka samu game da fim?

Nasara a harkar fim sai dai na yi wa Allah godiya, na ci arzikin fim, dan wataran ina tafiya a hanya sabida darajar fim da daukakarsa abubuwa da yawa an yi min saboda Allah, saboda fim. Saboda idan wasu sun gane ni a wani abun sai su yi min alkhairi. Na sha shiga Adaidaita Sahu mutane su kaunacen su biya min kudin.

Ko akwai wani kalubale da ki ka taba fuskanta cikin masana’antar?

Ba wani walubale dana taba fuskanta a ciki, shi fim idan ka ce za ka yi shi akwai wani abu wanda dole za ka yi hakuri, wanda yanayin fim din ne dole sai ka yi hakuri.

*Wane abu ne ya taba faruwa da ke na farinciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba a rayuwa?

Faranciki da bakin ciki yana nan a ranka, ba abun da ya kai rabuwa da iyaye, Astagafrillah Allah ne dai ya baka su ya karbi abinsa. Wannan abun shi ya fi taba ni, dan idan na tuna ba ni da uwa ba ni da uba duk abin da nake yi komai yana canjawa. Ko cikin farinciki nake, idan na tuna wannan ina jin komai yana canjawa. Sai na ji kamar na fi kowa maraici. Sai abun farinciki idan nayi tunanin Allah ya azurta ni da ‘ya’ya ina jin dadi ina jin sanyi a cikin zuciyata, ina kara godewa Allah.

Ko kina da ubangida a masana’anyar Kannywood?

Duk Kannywood ban da ubangidan da ya wuce Lawan Ahmad.

Kafin shigarki masana’antar Kannywood wadanne jarumai ne suke burge ki, kuma me ya sa?

Sani Danja, Lawan Ahmad, Uncle Sade S. Fulani kenan. A lokacin duna burge ni sosai har yanzu kuma. A mata kuma ina son Adaman Kamaye ina kaunarta, ina son Nafisa Abdullahi, ina son Rahama Sadau. Har yanzu ina kaunarsu, amma yanzu kowa ma yana burge ni.

Mene ne burinki na gaba game da fim?

Babban burina ina son Allah ya daukaka ni, na ga ni ma ina da abin da zan taimaki na kasa da ni.

Bayan fim kina wata sana’ar ne?

Ina siyar da shinkafa, ina yin ‘business’ wanda ya samu.

Misali wani daga cikin abokan aikinki ya ce yana sonki zai aure ki, shin za ki amince ki aure shi ko ba ki da ra’ayin auren d’an fim?

Tunda na yarda da aikin nawa babu batanci, kuma sana’ar mu daya da gudu zan yarda na aure shi, indai yana sona ina son shi.

Wasu na kokawa game da masana’antar kannywood, a takaice ya za ki yi wa masu karatu bayani game da masana’antar, shin wace ce Kannywood ya cikinta yake?

Kannywood masana’anta ce kamar yadda na yi miki bayani, duk yadda ka dauke ta haka za ta tafi da kai. Idan niyyarka daya sana’a ka dauke ta, Allah zai dafa maka. Idan kuma da wani manufa ka zo duk za ta tafi da kai. Ni dai gaskiya a sana’a na dauke ta, kuma Allah yana ba ni, ina samu daidai yadda sana’ar tawa ta ba ni.

Wane kira za ki yi ga masu kokarin shiga kannywood?

Kira na, dole ne su bi iyayensu in sun so su shiga, in kuma suna so su rarrashi iyayen nasu har su bar su tom, su shigo da kyakkyawan yakini sun fito sana’a.

Ko akwai wata shawara ko wani sako da ki ke da shi ga sauran abokan aikinki?

Shawara daya ce da Allah ubangiji ya hada kahunanmu, in an zo fadace-fadace in an zo a rika hakuri da juna, duk sana’ar da Allah ya hada ka da mutane sai ka yi hakuri da juna. Wataran za a yi maka ba dadi ka yi hakuri, wataran za a yi maka dadi dole ka karba ka yi farinciki. Kawai babban burina Allah ya hada kahunanmu, mu zama tsintsiya daya madaurinki daya. Gashi muna sana’a daya harkokinmu daya amman wani ya zagi wani ko wani abu bana fatan hakan, Allah ya kara hada kanmu. Allah kuma ya ba mu zaman lafiya, da daukaka mai amfani.

Me za ki ce da masoyanki masu kallon finafinanki?

Ba abin da zan ce da masoyana sai dai fatan alkhairi , ina gdoiya sosai Allah ya bar mu da masoyanmu da masu waunarmu. Ina yi wa kowa da kowa fatan alkhairi da masoyan da wanda ba masoyanma ina yi mana fatan alkhairi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu
Nishadi

Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu

November 13, 2025
Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala
Nishadi

Ta’aziyyar Rasuwar Jarumin Kannywood, Malam Nata’ala

November 8, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Nishadi

Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar

November 1, 2025

LABARAI MASU NASABA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

Duk Niyyar Da Mutum Ya Shigo Da Ita Kannywood Ita Za Ta Bi Shi —HAUWA KUJAMA

November 15, 2025
Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

Sin Ta Sha Alwashin Bunkasa Goyon Bayan Juna Tsakaninta Da Saliyo

November 15, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

Da Ɗumi-ɗumi: PDP Ta Kori Wike, Fayose, Anyanwu Da Wasu Mutane 7

November 15, 2025
An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka

November 15, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan 

November 15, 2025
Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

Illolin Neman Kudi Ido Rufe Ba Tare Da Kula Da Halal Ko Haram Ba

November 15, 2025
Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin

November 15, 2025
Yanzu Satar Da Kuka Yi Ba Ta Da Amfani: Kwankwaso Ga Gwamnonin APC

Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso

November 15, 2025
Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

Yadda Ake Miyar Margi (Margi Special)

November 15, 2025
Yadda Za Ku Gyara Kanku

Yadda Za Ku Gyara Kanku

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.