A yayin taron jagororin kungiyar BRICS da ya gudana ta kafar intanet a farkon makon nan, shugabannin kasashe membobin kungiyar sun gabatar da jawabai masu matukar fa’ida, musamman game da yadda za a hada karfi da karfe wajen ingiza nasarar hadakar, da cimma karin manyan nasarori.
Har ma a lokacin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwari uku da suka hada da martaba cudanyar mabanbantan sassa, da kare gaskiya da adalci. Sai kuma bukatar rungumar akidar yin komai a bude da cimma nasarar hadin gwiwar moriyar juna, da wanzar da tsarin gudanar da hada-hadar tattalin arziki da cinikayya. Da kuma nacewa hadin kai da hadin gwiwa, da dunkule karfin sassa daban daban domin cimma nasarar bai daya.
- Mele Kyari Ya Bayyana A Ofishin EFCC Kan Zargin Badaƙalar Dala Biliyan 7.2
- Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya
Ko shakka babu wadannan shawarwari na da matukar fa’ida ta fuskar karfafa kasuwanni, da hajojin sarrafawa da su kansu masana’antun sarrafa hajojin, da hadin gwiwa a fannin binciken kimiyya da fasaha da sauransu. Sun kuma dace da muradun hadakar BRICS na tafiya tare, da cimma moriyar bai daya ba tare da nuna wariya ba.
Har ila yau, karkashin wadannan shawarwari, kasashe membobin BRICS za su ci babbar gajiya daga fifikonsu, da ma alfanun dake tattare da hadakarsu wuri guda.
Zage damtse da kasashe membobin BRICS ke yi wajen karfafa cudanya, da hadin gwiwa na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da duniya ke fuskantar karin rashin tabbas, ake kuma kara fuskantar koma baya ta fuskar jituwa tsakanin wasu sassan kasashen duniya. Don haka, dandalin BRICS karin dama ce ga duniya ta rungumar juna, don kare cudanyar mabanbantan sassa, da tsarin cinikayya mai game dukkanin bangarori, har a kai ga cimma nasarar kafa al’ummar duniya mai makomar bai daya ga kowa da kowa.
Tarihi ya sha nuna yadda cudanyar sassa daban daban ke haifar da babbar gajiya ga daukacin bil’adama, don haka yayin da BRICS ke kara zamowa muhimmin jigo na ingiza dunkulewar sassan kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, kamata ya yi a ba ta goyon baya, ta yadda za ta daukaka muryoyin kasashe masu tasowa da masu samun saurin ci gaba. Ta haka ne kuma kungiyar za ta kara bunkasa gudummawarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da kawar da kariyar cinikayya, da kare muradun dukkanin sassan kasa da kasa ba tare da nuna bambanci ba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp