Yayin da matsalar rashin tsaro ke ci gaba da ta’azza a wasu yankunan jihar Zamfara, wasu mazauna yankunan sun bayyana mawuyaciyar rayuwar da rashin tsaro sakamakon ayyukan ta’addancin ‘yan bindiga ya jefa su.
Daga cikin wadanda jarrabawar ta shafa, sun ce “Sabida tsananin yunwa, da cin Dusa da Barace-barace muke rayuwa”
Yankunan da matsalar rashin tsaron tafi kamari a jihar, sun hada da: Magami da Dan Kurmi da ‘Yar Tasha da Dan Sadau da dai sauran wurare da dama.
A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da wani magidanci a jihar, ya bayyana cewa, “Ba ka isa ka taso daga Gusau ka nufi Magami ba, dole sai da rakiyar ‘yan sa-kai ko sojoji.
“Tsakanin Magami da Janguma, kilomita 25 ne kacal amma barazanar ‘yan bindiga da ke kan hanyar ta wuce misaltuwa”.