Sai dai, saboda tabbatar da hadin kan kasashen yankin, ECOWAS ta umarci mambobinta da su ci gaba da amincewa da fasfo din tafiye-tafiyen kasashen 3 da ke dauke da alamar kungiyar har sai abin da hali ya yi.
A yau Laraba, kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) ta amince da ficewar 3 daga cikin tsaffin mambobinta Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar daga cikinta, al’amarin da ya fara aiki tun daga 29 ga watan Janairun da muke ciki, bayan cikar wa’adin shekara guda da aka gindaya.
- Ba Za Mu Daina Kera Makaman Nukiliya Ba – Kim Jong Un
- Tafiye-Tafiye A Fadin Sin Ya Zarce Miliyan 300 A Rana Ta 4 Ta Hutun Bikin Bazara
A cikin wata sanarwa, hukumar ECOWAS ta kara da cewar kofofinta za su ci gaba da zama a bude domin karin tattaunawa da kasashen 3.
“Hukumar ta kafa wani tsarin da zai ba da damar tattaunawa game da wadannan tsare-tsare da kowace daga cikin kasashen 3. Wannan sako ya zama wajibi domin kaucewa rudani da katsewar rayuwa da harkokin al’ummominmu a wannan lokaci na sauyi,” kamar yadda sanarwar ta zayyana.
Kasashen 3 da ke karkashin mulkin soja sun sanarda ECOWAS a hukumance game da shirinsu na ficewa daga cikinta nan take a watan janairun 2024, inda suka kafa hujja da tsananin dogaron da kungiyar ke yi akan kasar Faransa.
Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Sahel” (AES).
Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata kungiyar Ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga kungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin kungiyar da kasashen guda uku, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga cigaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas.
A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da kungiyar Ecowas a hukumance dangane da bukatar ficewar tasu.
To sai dai bisa dokokin Ecowas, kasashen na bukatar sanar da kungiyar shekara guda kafin amincewa da ficewar.
Kuma a ranar Larabar nan ne wa’adin ke cika, bayan dukkan kasashen uku sun yi watsi da kiran kungiyar ta Ecowas na su kara tsawaita zamansu mambobinta na watanni shida domin samo mafita.
Yanzu dai kasashen na Burkina Faso da Mali da Nijar sun zama kawaye inda suka cure wuri guda karkashin kungiyar da suke kira Hadakar Kasashen Sahel (Allaiance of Sahel States (AES).
Shugabannin mulkin sojin kasashen dai sun zargi Ecowas da kakaba musu takunkumi na “rashin imani kuma haramtattu” bayan juyin mulkin da ya kawo su kan karaga.
Sun kuma yi amannar cewa kungiyar ta Afirka ta Yamma ba ta ba su cikakkiyar gudunmawa ba wajen yakar ‘yan’adda. Sun kuma yi amannar cewa Ecowas din ‘yar kanzagin tsohuwar uwar gijiyarsu ce wato Faransa.
Faransa ta kasance abokiyar hamayyar wannan kasashen da sojoji ke jagoranci da a yanzu haka suka kwammace yin hulda da kasashe irin su Rasha da Turkiyya da Iran.
‘ECOWAS ta raunana’
Kungiyar Ecowas dai ta samu rauni ne a watan Yulin 2023 bayan juyin mulkin jamhuriyar Nijar. Ecowas ta yi barazanar yin amfani da karfin soji wajen mayar da hambararren shugaban kasar, Bazoum Mohamed da kuma kakaba takunkuman tattalin arziki kan jamhuriyar wadanda yanzu duk an dage su.
Kasashen uku za su fito da nasu fasfo a ranar Larabar kuma sun sanar samar da rundunar sojin hadin gwiwa guda 5,000 da za su yaki masu ikrarin jihadi a yanki nan ba da jimawa ba.
Ficewar kasashen guda uku za ta yi wa Ecowas “illa musamman ta fuskarrikicin siyasa a yankin”, kamar yadda Gilles Yabi, shugaban kungiyar Wathi ta kwararru a Afirka ta Yamma, ya shaida wa AFP.
Hadakar kasashen guda uku na yankin Sahel, AES da wasu kasashen Ecowas na zaman tankiya. Misali Nijar ta ki amincewa ta bude iyakokinta ga jamhuriyar Benin wadda take zargi da bai wa ‘yanta’adda mafaka inda suke yin atisaye. Ta kuma zargi Nijeriya da kasancewa wani “filin daga na bayan gida” da ka iya yi mata illa.
Dukkanin kasashen biyu na Benin da Nijeriya sun musanta zarge-zargen makwabciyar tasu.
Togo da Ghana na zawarcin kungiyar AES
Kasar Togo ta kasance wadda ta bude tashar jirgin ruwanta ga kasashen uku na AES sannan kuma tana kokarin shiga tsakani.
“Togo tana da mafarki mai gajeren zango bisa hasashen da ake da su da suka shafi muradun tattalin arziki da zai illata Ecowas,” in ji Yabi.
Ministan harkokin wajen Togo a baya-bayan nan ya fadi cewa ba su cire ran cewa kasar tasa za ta shiga kungiyar ta AES ba.
Idan Ecowas ta rasa mamba ta hudu kamar Togo wadda ke da hanyoyin sufuri na ruwa, “za mu mamakin yadda Ecowas za ta rayu”, in Rinaldo Depagne, mataimakin darektan Afirka a kungiyar wanzar da zaman lafiya ta kasa da kasa ta ICG.
AES “na kakarin gamsar da kasashe cewa Ecowas ba ta yin komai sannan za su iya maye gurbinta,” in ji wata majiyar huldar jakadanci. “Sun fahimci cewa ba za su iya rayuwa su kadai ba.”
Ghana karkashin sabon shugaban kasarta, John mahama tana kokarin kai wa ga kasashen na AES. Dramani Mahama ya gana da shugabanninta sannan ya sanar cewa zai aike da jakadan na musamman zuwa kungiyar.
“Sabon shugaban kasar ya banbanta da mutumin da ya gada dangane da matsayar Ghana kan juyin mulkin da kasashen suka yi,” in ji Depagne na ICG.
“Tambayoyin da ake yi su ne ko za mu iya kasancewa a kungiyar AES da kuma Ecowas a lokaci guda?”
‘Sabuwar ECOWAS’
Abin da ya faru ya janyo muhawara kan bukatar kungiyar ta Ecowas “ta sake komawa ga muradunta na asali kan tattalin arziki da doka da dimokradiyya,” in ji Yabi.
“Kowa na sane da irin bukatar yin sauyi ga Ecowas domin cimma kungiyar Ecowas ta jama’a,” in ji wani minista na daya daga cikin kasashen Afirka ta yamma wanda ke tattaunawa da shugabannin mulkin sojin AES.
“AES ka iya zama tamkar dakin gwaji kuma za ta iya ci gaba da kasancewa mamba amma a sabuwar kungiyar Ecowas,” ya yi karin haske.
Duk da raunin da Ecowas din ta samu, Yabi ya ce dole ne mu karfafa dangantaka tsakanin kasashen AES da na Ecowas domin ” ci gaba da alakar tattalin arziki” sannan kuma mu fuskanci matsalar tsaro.
Masu ikrarin Jihadi sun haddasa mutuwar dubban jama’a a Mali da Nijar da Burkina Faso a tsawon shekaru 10 da suka gabata, sannan kuma rikicin ya fantsama zuwa kasashen kungiyar Ecowas kamar Benin da Togo.