A wani yunkuri na tabbatar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afitka, ECOWAS, ta yanke shawarar janye takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa jamhuriyar Nijar, da Mali da kuma Guinea-Bissau.
An cimma wannan matsaya ne a yayin wani taro na musamman da ya shafi zaman lafiya, siyasa, da tsaro na kasashen ECOWAS, wanda aka gudanar a yau Asabar a Abuja.
ECOWAS ta yanke shawarar dage wasu takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa Guinea. Bugu da kari, an kuma sassauta takunkumin da aka kakabawa kasar Mali a wani bangare na kudurin.
Cikakkun bayanai daga baya…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp