BBC ta rawaito cewa, Ƙungiyar ƙasasahen yammacin Afirka ECOWAS ko CEDEAO, za ta gudanar da taron ƙoli a babban birnin Nijeriya, Abuja a ranar Alhamis domin tattauna batun Nijar, inda aka yi juyin mulki.
A ranar Lahadi jagororin juyin mulkin suka yi watsi da wa’adin da ECOWAS ta ba su na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki, ko kuma su fuskanci matakin soji.
Ƙasahen Burkina Faso da Mali sun ce za su tura tawagar haɗin gwiwa domin nuna goyon baya zuwa Nijar.