• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

EFCC Ba Samame Ta Kai Mana Ba – Dangote

by Sulaiman
2 years ago
Efcc

A ƙarshe, Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya yi ƙarin haske kan ziyarar da jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Tu’annati (EFCC) suka kai babbar hedikwatar kamfanin na baya-bayan nan, kuma ya ba da tabbacin cewa, kamfanin zai taimaka wa hukumar wajen gudanar da bincike.

Jami’an EFCC sun ziyarci hedikwatar rukunin Dangote ne da ke Legas kan bayanan kuɗaɗen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ware mata daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

  • Rasha Ta Harba Makamai Masu Linzami Fiye Da 500 Kan Yukiren
  • EFCC Ta Gurfanar Da Ma’aurata Kan Damfarar Miliyan 410 A Kano

Kwanaki bayan ziyarar, Dangote a wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya bayyana cewa, “Kamar yadda aka yi ta yaɗa rahotannin ziyarar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi zuwa babban ofishin mu da ke Jihar Legas a ranar 4 ga watan Janairun 2024, mun fahimci irin karsashin da abokan hulɗar mu da kuma sauran al’umma su ke da shi domin sanin haƙiƙanin abin da ya faru, hakan ne ya sa za mu sanar da ku haƙiƙanin abin da ya faru.

“A ranar 6 ga watan Disamba, 2023 mun samu wasiƙa daga Hukumar EFCC, inda ta bukacibmu ba su ba’asin kuɗaɗen waje (Dalar Amurka) da CBN ya ba mu daga shekara 2014 zuwa yanzu. Mun fahimci cewa ba mu kaɗai aka baiwa wannan wasiƙar ba, an turawa wasu kamfanonin kimanin 51 irin wannan wasiƙar kuma suma ana neman wannan bayanin daga gare su,” inji sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mun baiwa Hukumar EFCC takardar karɓar buƙatar da suka turo mana, muka kuma buƙaci su yi mana ƙarin bayani a ɓangaren da suke buƙatar bayani, ko kuma daga wane ɓangare na rukunin kamfanonin mu. Mun kuma buƙaci ƙarin lokaci domin haɗawa tare da gabatar musu takardun da suka kai shekaru goma.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

“Duk da cewa, hukumar EFCC ba su fayyace mana ɓangaren da suke da buƙatar bayanan ba, kuma ba su bamu damar da muka buƙata daga gare su ba dangane da ƙarin lokaci, suka kafe akan lallai suna da buƙatar wannan bayanai a ƙurarren lokaci, amma mun tabbatarwa hukumar EFCC cewa za mu gabatar musu da bayanan da suka buƙata a lokuta daban-daban saboda muna kan kammala tattara bayanan.”

Sanarwar ta cigaba da cewa, “A ranar 4 ga watan Janairu 2024, ma’aikatan mu suka fara miƙawa Hukumar EFCC rahoto kashi na farko. Baya ga haka, jami’an hukumar EFCC suka ƙi karɓar takardun rahoton da muka gabatar musu, suka ƙi amincewa da kai musu da aka yi, suka nace akan dai su zo ofishin mu su karɓi wannan kwafin rahoton da muka gabatar musu da kansu.

“Duk da kasancewar ma’aikatan mu suna ofishin su da takardun bayanan da suka buƙata, wasu daga cikin jami’ansu suka wuce zuwa ofishin domin karɓar wannan rahoton da aka gabatar musu wanda hakan ya zubar mana da kima da kuma taɓa darajar mu. Bugu da kari, jami’an nasu ba su ɗauki wasu takardu ko kuma wani kundi daga ofishinmu ba a yayin da suka kawo ziyarar ofishinmu ba, domin duk abinda suke nema yana ofishinsu.

“Muna faɗa da babbar murya cewa, babu wani zargi ko kuma wata badaƙala da ake zargin ɗaya daga cikin rukunin kamfaninnikan lmu da ita a wannan lokacin, face dai muna bayar da bayanan da aka buƙata daga gare mu domin taimakawa hukumar EFCC a binciken da ta ke yi.

“A matsayinmu na kamfanin da ya ke biyayya ga dokokin ƙasa, a shirye muke da mu ba da haɗin kai wajen bai wa hukumar EFCC duk wani bayani da suke da buƙata daga wajen mu. Mun riga mun miƙa musu kason farko na bayanan da suka buƙata daga gare mu, muna kuma aiki tuƙuru domin ganin mun ba su sauran bayanan da suka rage daga gare mu akan lokaci, domin taimakawa binciken da suke yi.

“Gamayyar Kamfanonin mu suna daga cikin waɗanda suka fi bada gudunmawa wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar nan, kuma ɗaya cikin manyan kamfanonin da ke kasuwar hannayen jarin ƙasar nan, sannan kuma ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da suka fi biyan haraji mai yawa a ƙasar nan. Mun kasance masu biyayya ga dokokin ƙasa tare da kare martabar ta a yunƙurin da Gwamnatin Tarayya ta ke yi na ganin an samar da bunƙasar tattalin arziki ta yadda masu zuba hannayen jari na gida da na waje za su samu damar yin hakan”, inji sanarwar.

A ƙarshe, sanarwar ta ce, “Muna kira ga abokan hulɗarmu su fahimci yadda abin yake, su kuma kwantar da hankulansu. Za mu ci gaba da sanar da su duk halin da ake ciki lokaci-zuwa-lokaci.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Asuu
Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro
Labarai

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
majalisar kasa
Labarai

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
Next Post
Nijeriya Da Guinea Za Su Buga Wasan Sada Zumunta A Dubai

Nijeriya Da Guinea Za Su Buga Wasan Sada Zumunta A Dubai

LABARAI MASU NASABA

Asuu

Gwamnatin Tarayya Ta Saki Naira Biliyan 2.3 Ga ASUU

October 29, 2025
Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

Sabon Ingantaccen Hadin Gwiwar “Sin-ASEAN 3.0″ Ya Kafa Sabon Misali Na Hadin Kan Yanki

October 29, 2025
Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

Sulhu Da ’Yan Bindiga Ba Tare Da Sun Ajiye Makamai Ba Tamkar Miƙa Wuya Ne – Gwamna Lawal ga Hukumomin Tsaro

October 29, 2025
An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

An Yi Taron Tataunawa Tsakanin Kasa Da Kasa A Moscow, Manama, Da Budapest

October 29, 2025
majalisar kasa

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Amso Bashin Dala Biliyan 2.34 A Kasuwar Jari Ta Duniya

October 29, 2025
An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin

October 29, 2025
Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

Kotu Ta Umarci Ƙwace Dala 49,700 Daga Tsohon Jami’in INEC

October 29, 2025
Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

Yadda Kasar Sin Ke Kara Kyautata Tsarin Kare Muradun Al’umma A Bangaren Shari’a

October 29, 2025
COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.