Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya misalta ikirarin mawaki, Femi Kuti, da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta taba gayyatarshi kan zarge-zargen damfara da zamba bayan kammala wa’adin mulkinsa a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bayelsa a matsayin ‘tsagoran karya, shaci-fadi’ ne kawai.
A kwanakin baya ne dai mawakin ya yi zargin cewa Jonathan ta taba kasancewa a karkashin tambayiyin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa bisa zargin da suka shafi rashawa, sai dai a bayanin da Jonathan din ya fitar ya bayyana wannan zargin a matsayin karya ne kawai.
- “Ka Da Ku Kuskura Ku Zaɓi Masu Kashe Mutane A Zaɓen 2023 — Goodluck Jonathan
- Ba Na Iya Barci Saboda Matsalar Tsaro Lokacin Da Nake Mulki –Jonathan
Jami’in yada labarai na ofishin tsohon shugaban kasan, Wealth Dickson Ominabo, ya karya batun a wata sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a.
Ya ce, zargin na Kuti ba zai rasa nasaba da bayanan da wasu ‘yan siyasa ke yadawa domin karkatar da hankalin jama’a da yada labaran kanzon kurege a cikin jama’a domin cimma wata manufa.