Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya bayyana cewar ba ya yin barci sakamakon matsalar tsaro da ta addabi kasar nan a lokacin da yake shugabanci.
Jonathan ya shaida hakan ne a Jalingo lokacin da yake kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin Jihar Taraba karkashin gwamna Darius Ishaku ta samar.
- Jam’iyyar Labour Ta Yi Fatali Da Hukuncin Da Kotu Ta Yanke Kan Zababben Gwamnan Abia
- Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari
Da yake jawabi lokacin kaddamar da tawayen hanya mai nisan kilomita 22 da ya tashi daga Panti Napo zuwa sansanin ‘yan yi wa kasa hidima (NYSC), tsohon shugaban kasan ya jinjina wa al’ummar jihar a bisa rungumar zaman lafiya da suka yi.
Kazalika, ya yaba wa gwamnan da dan kwangilar da ya kula da aikin, kamfanin Claneburge bisa gudanar da nagartaccen aiki.
Ya ce “Lokacin da nake shugaban Nijeriya, matsalar tsaro ta sanya ko barci ba na iya yi da daddare, wasu lokutan ko ina coci, ADC dina zai kawo waya ya nuna min yadda aka kashe mutane ko aka yi garkuwa da su, wannan lamarin ya yi matukar ba ni ciwon kai ya tada min hankali.
“A lokacin da na sauka a filin jirgin saman Jalingo, na ga daraktan hukumar tsaron farin kaya ta SSS nan da nan na masa tambayar cewa ya matakin tsaro yake a Jihar Taraba, ya amsa min da cewa Taraba akwai cikakken tsaro.
“Na yi imanin cewa matsalar tsaro na hannun mutane, idan kuma suka so za a zauna lafiya, don haka ina yaba wa mutanen Taraba da kuka zabi ku zauna cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, batun tsaro ba lamari ne na Gwamnatin tarayya da jihohin zalla ba, a’a lamari ne da ya shafi kowa. Ina gode muku da kuka zabi zama cikin lafiya,” ya shaida.
Shi kuma gwamna Ishaku ya ce, samar da aikin na daga cikin manufofin gwamnatinsa na kyautata wa al’umma ne, ya gode wa Allah da ya bashi damar gudanarwa da karasa aikin har ma aka kaddamar.