Kwamandan Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa zagon kasa (EFCC) na shiyyar Ilorin, Michael Nzekwe, ya bayyana kudurin hukumar na hada kai da rundunar sojin Nijeriya wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu daukar nauyin ta’addanci a kasar nan.
Nzekwe ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci rundunar soji ta 22 Armored Brigade dake Barikin Sobi a Ilorin ta jihar Kwara.
“Ziyararmu ta zama wajibi, kasancewar rundunar soji ta kasance mai ruwa da tsaki ce itama a yaki da cin hanci da rashawa da yaki da masu daukar nauyin ta’addanci, wanda wannan wani babban bangare ne na aikinmu.
“Don haka ya zama wajibi mu hada kai da Sojojin Nijeriya domin kawo karshen cin hanci da rashawa a Nijeriya ta hanyar ganowa da kuma yanke hanyoyin samun kudade ga ‘yan ta’adda,” in ji Nzekwe.
A nasa jawabin, Kwamandan Barikin, Birgediya-Janar Adebayo Babalola, ya yabawa matakan da hukumar EFCC ta dauka, inda ya kara da cewa rundunar sojin Nijeriya za ta ci gaba da karfafa alaka da hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kokarinta na tsaftace kasar daga cin hanci da rashawa.