Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa (EFCC) ta kama babban Akanta-janar na jihar Bauchi, Alhaji Sirajo Mohammed Jaja, kan zargin almundahanar naira biliyan 70.
Binciken Jaridar LEADERSHIP ya nuna cewa an kama Jaja ne a ranar Laraba a Abuja tare da wasu mutum biyu, Aliyu Abubakar na kamfanin Jasfad Resources Enterprise, a bangaren canjin takardun kudi (BDC) da kuma Sunusi Ibrahim Sambo, mai hada-hadar kuɗaɗen ta na’urar (PoS).
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 10, Sun Ceto Mutane 101 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina Da Zamfara.
- Ribas: Fubara Ya Fice Daga Gidan Gwamnati Yayin Da Sabon Shugaba Ke Shirin Karɓar Mulki
Dukkaninsu sun shiga hannu ne bisa binciken da ake yi na sama da faɗi, karkatar da dukiyar al’umma, da kuma janyo salwantuwar kuɗade da ya kai Naira biliyan 70.
Wani ƙarin zance kan batun, an gano hukumar na kuma bincikar gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad dukka da hannu kan wannan lamarin.
Tuni dai bincike ya nuna cewa, an fitar da tsabar kudi naira biliyan 59 ta asusun bankuna daban-daban da babban akantan ya buɗe kuma yake gudanar da su a madadin gwamnatin jihar.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan.
An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi.
A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp