Daya daga cikin wadanda ake zargi da sayan kuri’un sun boye Atamfofi a wurin ajiye kaya na mota kira Peugeot 406.
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, (EFCC), karkashin jagorancin Kwamandan EFCC, Aliyu Yusuf, a ranar 25 ga Fabrairu, 2023, sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da sayan kuri’u a Gusau, Jihar Zamfara.
- Yadda Jami’an EFCC Suka Yi Dirar Mikiya A Rumfunan Zabe A Zamfara
- EFCC Ta Kama Wasu Masu Sayen Katin Zabe A Kano, Kaduna Da Abuja
Inda aka kama Mustapha Abubaka da kudi N107,000 (Naira Dubu Dari da Bakwai) da tikitin da aka kera na musamman domin masu kada kuri’a a matsayin shaida na zaben jam’iyyarsa, kafin karbar kudaden, an kama Isa Abdullahi da laifin sayan kuri’u tare da boye su a cikin boot da kujerar baya na Peugeot 406.
Wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kwato suna hannun hukumar yayin da ake ci gaba da bincike.