EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da sayan kuri’u a Kwara
Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) a Ilorin, Jihar Kwara, a ranar Asabar, sun kama wasu mutane 20 da take zargi da sayan kuri’u a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki a jihar.
Jami’an sun kama wadanda ake zargin ne a karkashin jagorancin ACE Michael Nzekwe.
Hukumar ta bayyana hakan ne shafinta na sada zumunta na manhajar WhatsApp.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp