Reshen shiyyar Ibadan na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a ranar Laraba ta cafke mutum 39 da take zargi da damfara a yanar gizo a Ibadan, jihar Oyo.
Wadanda ake zargin, sun yi ikirarin cewa su dalibai ne a manyan makarantu daban-daban.
Kazalika, bayan binciken da aka gudanar a wayoyin wadanda aka kaman an gano takardu da sakonnin damfara na bankuna.
Wadanda aka kaman su ne: Okeowo Abiodun Akeem, Yekini Ismail Omokayode, Odediran Abdulfatahi Dolapo, Isiaka Olumide Hammed, Obioma Honour Umaduabuchi, Olorunsola Eniola Johnson, Olabiyi Ifeoluwa Joseph, Razaq Adams Lekan, Oladimeji Abdulrahmon Olamide, Oyelaran Olayiwoola Jeremiah, Patrick Simon, Adefowora Omotayo David, Adediran Qudus Wale, Onipede Damilola Zacheaus, Ajayi Ifedolapo Oluwatofunmi, Oluwole Ayomide Oluwasegun, Usman Mubarak Oluwadamilare, Dapo-Ajayi Temitope Faith, Diyaolu Olamide Samuel, Ugbama Daniel Efemena da kuma Ayoade Taofeek Adekunle.
Sauran su ne: Egberongbe Adebayo Adedamola, Ajadi Ayinla Ibrahim, Ajeigbe Christian Toluwase, Alabi Daniel Oluwatosin, Olawooyin Taoheed Olakunle, Oguntuase Tope Francis, Salami Adam Akanfe, Olanrewaju Michael Damola, Kareem Afeez Alabi, Onuma Chidubem Williams, Rasaq Sodiq Olamilekan, Okusanwo Mayowa Daniel hadi da Wahab Adebayo Abdullahi.
An kamasu tare da manyan motoci guda biyar, wayoyin hannu masu tsaida, na’ura Mai kwakwalwa(Laptops) tare da wasu abubuwan.