Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana damuwa kan yadda damfara da sunan zuba jari da kuɗaɗe na zamani (virtual assets) ke ƙara yaɗuwa a faɗin Afrika, yana mai bayyana hakan a matsayin babbar barazana ga tattalin arziƙi da amincin jama’a.
Da yake jawabi a ranar Alhamis a bikin ranar yaƙi da cin hanci ta tarayyar Afrika (AU Anti-Corruption Day) da aka gudanar a Otal ɗin Sinclair, Ilorin, jihar Kwara, Olukoyede wanda ya samu wakilcin Daraktan EFCC na yankin Ilorin, Mr. Daniel Isei, ya ce masu damfara na amfani da fasahar zamani domin yaudarar masu neman riba cikin gaggawa ta hanyar zuba jari da daɗin bakin cewa za’a samu riba mai yawa.
- EFCC Ta Kama Ƴan Ƙasashen Waje 146 Kan Laifukan Zambar Kuɗaɗe
- Ni Ne Na Kai Kaina ga Hukumar EFCC, In Ji Tsohon Jami’in NNPC
Ya bayyana cewa da dama daga cikin masu amfani da crypto da wasu kuɗaɗe na zamani ba lallai ne su zama masu laifi ba, amma fasaharsu tana ta zama kayan aiki ga masu aikata laifukan kuɗi da na damfara.
Olukoyede ya ce bincike ya nuna cewa wasu ƴan siyasa da ɓarayin gwamnati na amfani da wallet ɗin crypto domin ɓoye kuɗaɗen sata don kauce wa ganowa. Haka kuma, ya ja hankalin jama’a kan yawaitar shafukan zuba jari na bogi da ke amfani da kuɗin intanet domin jawo masu zuba jari da alƙawarin samun gagarumar riba cikin sauri.
A nasa ɓangaren, James Allison, wani babban jami’in EFCC, ya gabatar da jawabi kan dabarun da masu damfara ke amfani da su wajen amfani da crypto, NFTs da sauran kuɗaɗen na zamani don cutar da jama’a. Ya bayyana yadda rashin fahimtar tsarin kuɗaɗen na zamani ke barin ƴan Nijeriya cikin haɗarin faɗawa tarkon masu damfara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp