Jami’an Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Nijeriya EFCC sun kama shugaban wata coci a Jihar Ebonyi, bisa zargin yi wa mabiya cocinsa da ‘yan Nijeriya zamba na tallafin kudin bogi daga wata gidauniya, wanda kudin ya kai Naira biliyan 1,319,040,274.
Wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a yau ta ce an kama faston kan zargin damfarar wadanda tsautsayi ya fada mawa da suka hada da kungiyoyi masu zaman kansu na Nijeriya da daidaikun mutane, ta hanyar tallata wani aiki da ake neman tallafi na kungiyarsa.
Haka kuma EFCC din ta yi zargin cewar ya nemi wadanda lamarin ya shafa da su yi rajista tare da biyan kudin yin rajista, inda ya karbi Naira milyan 1,800,000 daga hannun kowannen su, inda ya tara kudin da suka kai sama da Naira biliyan daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp