Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta kwace fasfo ɗin tsohon gwamnan jihar Delta, Okowa bisa zargin karkatar da kuɗin jihar da ya kai Naira Tiriliyan 1.3.
Hukumar EFCC dai ta tsare tsohon gwamnan ne a ranar 4 ga watan Nuwambar wannan shekarar da muke ciki, wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya, kuma jigo a jam’iyyar PDP, Atiku abubakar ya musanta tuhumar da ake masa.
- ‘Yan Bindiga Sun Bude Wa Tawagar Jami’an Tsaron Okowa Wuta Sun Kashe ‘Yansanda Uku
- Okawa Bai Taimake Ni Da Kuɗin Jihar Delta Don Na Yi Kamfe A 2023 Ba – Atiku
An sake shi ne bayan da ya cika sharuɗɗan beli, ciki har da mika fasfo ɗinsa.
Da yake mayar da martani kan zarge-zargen, Okowa ya bayyana su a matsayin yarfen siyasa da kuma ƙoƙarin ganin an ɓata shi a idon duniya.
Okowa ya ce ya hidimtawa jiharsa bisa gaskiya da riƙon amana a lokacin da yake gudanar da mulkinsa.