Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta ce, ta samu izinin kama tsohuwar ministan albarkatun Mai, Diezani Alison-Madueke.
Hukumar ta kuma sanar da cewa, ta fara shirye-shiryen taso keyar Diezani daga can Birtaniya zuwa gida Nijeriya.
- Zargin Bi-ta-da-ƙulli: An Hana Kotun Ɗa’ar Ma’aikata Da EFCC Da ICPC Ci Gaba Da Binciken Shugaban Yaƙi Da Rashawa Na Kano
- EFCC Da CCB Sun Gayyaci Muhyi Magaji Rimin Gado
Rahotonni sun ce, tsohuwar ministar ta bayyana a kotun majistire ta Westminster da ke kasar Landan a ranar Litinin dangane da zargin cin hancin fam dubu 100,000.
Alkalin kotun, Michael Snow, ya amince da bayar da belin Alison-Madueke kan fam 70,000 kuma a biya nan take tare da kakaba mata wasu sharuda da suka hada da hana ta fita daga karfe 11 na dare zuwa 6 na safiya sannan kuma za a makala mata na’urar tsaro a kafarta da za ta kai rahoto kai tsaye ga jami’an tsaro da zarar ta tsallake sharuddan da kotun ta gindaya mata.
EFCC, a wata sanarwa da mukaddashin shugaban sashin yada labarai, Dele Oyewale, ya fitar, ta ce, “gurfanar da tsohowar ministan, nasara ce matuka dangane da tuhume-tuhumen zargin cin hanci da rashawa da ake mata.
“Duk da cewa tuhume-tuhumen da kotun London ke mata, gaba daya sun sha banban da wadanda EFCC ke mata har guda 13 da suka shafi sama da fadi da dukiyar al’umma, yana da kyau a lura da cewa dukkanin wani aikin laifi sunansa laifi, kuma ba tare da wani banbanci ba, babu wani laifi da zai tafi ba tare da an hukunta wanda ya aikata ba.
“Tuhume-tuhumen da EFCC ke wa Madueke sun shafi irin wanda ake mata a Dubai, Birtaniya, Amurka da kuma na Nijeriya.
Alison-Madueke, ‘yar shekara 63 a duniya, ta kasance wata jigo a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Ta yi aiki a matsayin ministan albarkatun mai daga 2010 zuwa 2015 kuma ta taba zama shugaban kungiyar kasashe masu arzikin danyen mai na duniya (OPEC).