Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) da Code of Conduct Bureau, (CCB), sun gayyaci shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, domin amsa tambayoyi kan kudaden hukumar.
Kwanan nan Rimingado ya ce ya gudanar da binciken kwakwaf kan faifan bidiyo da ke nuna tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, yana karbar wasu makudan daloli da ake kyautata zaton cin hanci ne.
- Matasa Ku Rungumi Sana’ar Noma Domin Magance Matsalar Yunwa – Gwamnan Neja
- Mutane 12 Sun Mutu, 80 Sun Jikkata A Bikin Bude Wasanni A Madagascar
Gwamna Ganduje ya samu umarnin wucin gadi da ya hana hukumar gudanar da bincike a kansa, da iyalansa da kuma duk wani mai rike da mukaman siyasa a mulkinsa.
Sai dai a wani abin da ake ganin ana takun saka da Gwamna Ganduje, a lokaci guda EFCC da CCB sun kaddamar da bincike kan ayyukan Rimingado a hukumar.
Wasikar EFCC mai dauke da kwanan wata 8 ga watan Agusta, 2023, ta ce: “Hukumar na binciken wani lamari da bukatar samun wasu bayanai daga ofishinku wanda ya zama wajibi.
“Bisa la’akari da abubuwan da ke sama, ana bukatarku da ku ba wa Daraktan Kudi da Akanta don bayar da rahoto da tattaunawa kan wasu bayanai:
“Cikakkun bayanai game ofishin Akanta Janar na jihar Kano ya fitar a ofishinku daga shekarar 2019 zuwa 2021.”
A hannu guda kuma, wasikar ta CCB, mai kwanan wata 16 ga watan Agusta, 2023, tana neman Mista Rimingado da ya bayyana bayanan wasu kudade da hukumarsa ta kwato daga shekarar 2016 zuwa yau.