Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su rungumi haɗin kai da zaman lafiya.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Asabar, ta taya al’ummar musulmi murnar zagayowar Ƙaramar Sallah, wanda ke nuna kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.
- Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah
- Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Fiji: Ya Kamata A Koyi Fasahohin Da Kasar Sin Ta Samu A Fannin Raya Kasa
Ya buƙaci al’ummar Musulmin Jihar Zamfara da sauran jihohi da su yi amfani da sadaukarwar da suka yi ga Allah a cikin watan Ramadan.
Ya ce: “Ya ‘yan uwa Musulmi na Jihar Zamfara da ma sauran wurare, ina miƙa saƙon barka da Sallah tare da taya mu murnar kammala azumin shekarar Hijira ta 1446, wannan wata mai alfarma ta kasance lokaci na sadaukarwa ga Allah (SWT).
“Yayin da muke gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu da ya ci gaba da ayyukan ƙwarai, da haƙuri, da karamcin da aka yi a watan Ramadan.
“Ƙalubalan da ke gabanmu suna da yawa kuma suna buƙatar haɗin kai don ganin an magance su, don haka mu ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu yi aiki tare a matsayin al’umma ɗaya, mu goyi bayan ajandar gwamnati na ceto da sake gina jiharmu.
Gwamna Lawal ya kuma yaba da ƙoƙarin shugabannin addini da na al’umma bisa yadda suke ci gaba da jajircewa wajen samar da zaman lafiya da inganta ɗabi’un da haɗin kan mutane wuri guda.
“Yayin da muke taruwa da masoyanmu domin gudanar da bukukuwan murnar wannan rana, mu sanya jiharmu cikin addu’o’in neman taimakon Ubangiji yayin da muke aiki ba dare ba rana don magance ɗimbin ƙalubalen da ke addabar jihar, Allah SWT ya karbi ibadun mu, ya gafarta mana kurakuran mu, ya kuma albarkaci jiharmu da kasa baki ɗaya tare da samun dawwamammen zaman lafiya da wadatar tattalin arziki. BARKA DA SALLAH”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp