A yau Lahadi, 26 ga watan Oktoba, za a sake samun babban karo tsakanin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya — Real Madrid da Barcelona, a filin wasa na Santiago Bernabeu dake birnin Madrid, ƙasar Sifaniya. Wannan wasa, wanda ake kira El Classico, yana daya daga cikin wasannin da ke ɗaukar hankalin masoya ƙwallon ƙafa a duk duniya saboda tarihi da kuma ƙarfin ƙungiyoyin biyu.
El Classico ba kawai wasa bane, alama ce ta karawar tarihi tsakanin birane biyu — Madrid da Barcelona — waɗanda ke wakiltar siyasa, da tarihi, da al’adu daban-daban na Sifaniya. Duk lokacin da ƙungiyoyin suka haɗu, ana ganin shi tamkar fafatawar kimar kungiya da girman tarihi. Sau da dama nasarar wannan wasa kan zama alamar wanda zai fi tasiri wajen lashe gasa ta La Liga a karshen kakar wasa.
- Mbappe Ya Jefa Kwallonsa Ta 60 A Gasar Zakarun Turai A Wasan Da Real Madrid Ta Doke Kairat
- Zuwan Tsoffin ’Yan Wasan Barcelona Abuja Ya Nuna Ana Samun Zaman Lafiya A Nijeriya – Matawalle
Wasan na yau shi ne karo na 268 a tarihin haɗuwarsu, kuma ya zo ne a wani lokaci da Real Madrid ke saman tebur da maki 24, yayinda Barcelona ke biye da maki 22. Wannan ya ƙara zafafa wasan, domin nasarar kowace ƙungiya na nufin matsayi mai muhimmanci a fafutukar neman kambun La Liga.
A tarihi, ƙungiyoyin biyu sun buga wasanni 263 a hukumance, inda aka yi canjaras sau 53, Barcelona ta samu nasara 107, haka nan Real Madrid ma ta samu 107 — abin da ke nuna irin daidaiton ƙarfin da ke tsakaninsu tsawon shekaru. Wannan ya sa kowane karo na El Classico ke zama sabon tarihi da ke iya sauya alƙiblar gasar.
Masu sharhi na wasanni sun bayyana cewa wasan na yau zai kasance mai cike da fasaha da ƙwarewa, musamman ganin cewa kungiyoyin biyu na da ƴan wasa matasa masu zafin gwuiwa kamar Vinicius Jr., da Jude Bellingham, da Lamine Yamal, waɗanda ke son rubuta sunayensu cikin jerin manyan taurarin da suka taba buga El Classico. Dukkan idanu yanzu sun karkata zuwa Madrid, inda ake jiran ganin wanda zai yi nasara a wannan karon.














