ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

El-rufa’i Ba Zai Halarci Taron Jam’iyyar APC Na Kasa Ba, Kuma Ganduje Na Nan A Shugabanci 

by Sulaiman
10 months ago
El-rufa'i

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya taron kwamitin zartaswa na kasa wanda ake sa ran za ta yi ranar Laraba, jam’iyyar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na iya neman shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa.
Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya karyata jita-jitar a wata hira da aka yi da shi, inda ya jaddada cewa, jam’iyyar ta saba gudanar da irin wannan taron, ba wai sai don shirin zabe ba.
  • Amurka Za Ta Illata Kanta Bisa Tsara Matakan Kayyade Samar Wa Sin Sassan Na’urorin Laturoni Na Semiconductor
  • Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa
A halin da ake ciki, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon ministan birnin tarayya, Nasir El-Rufai, ya tabbatar da cewa ba zai halarci taron jam’iyyar na kasa ba a yayin da yake magana a shirin ‘PrimeTime’ na Arise Television a daren ranar Litinin, inda ya bayyana rashin sanar da shi a matsayin dalilin rashin halartarsa.
“Ba zan samu halartar taron kolin jam’iyyar APC na kasa ba. Zan koma birnin Alkahira, inda nake shafe yawancin lokaci na. Ban sami isasshiyar sanarwa ba. Kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu ya bayar da kwanaki 21, ko kuma kwanaki 14 don samun sanarwar gudanar da irin wannan taron. Ba na tsammanin an turo min da gayyatar,” in ji shi.
Ya ci gaba da bayyana cewa, “Idan ya kasance, ban samu gayyatar makonni biyu zuwa makonni uku da suka gabata ba. Don haka, ina da tsare-tsare na, kuma gobe zan tafi. Amma abokaina da yawa za su halarta, don haka ba zan rasa kome ba. Zan san abin da aka tattauna.”
Babban taron dai, zai kasance karkashin jagorancin shugaba Tinubu, inda ake sa ran mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari za su halarta. Haka kuma akwai shugaban majalisar dattawa Dr. Godswill Akpabio, gwamnonin jam’iyyar APC na baya da na yanzu, tsoffin shugabannin majalisar wakilai da masu rike da madafun iko, shugabannin jam’iyyar na jihohi, kwamitin ayyuka na kasa, da sauran masu ruwa da tsaki.
ADVERTISEMENT
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja
Manyan Labarai

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta
Manyan Labarai

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Next Post
Gwamna Aliyu Ya Tsige Hakimai 15 Na Sokoto

Gwamnatin Sokoto Za Ta Kashe Naira Miliyan 998 A Cibiyoyin Ciyarwa Na Ramadan

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.