Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar Kula da Ƴansanda kan zargin wasu jami’an ƴansanda a jihar da cin zarafi da kuma amfani da muƙaminsu ba bisa ƙa’ida ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafin X, El-Rufa’i ya ce abin da ya kai ƙorafi ya haɗa da aikata rashin ƙwarewa da kuma karya dokar Ƴansanda ta shekarar 2020.
- Kasar Sin Ta Zama Wurin Da Aka Fi Zaba Domin Warware Takaddamar Cinikayya Da Ta Shafi Kasa Da Kasa
- Sin Ta Gabatar Da Sabon Injin Aiki A Manyan Na’urori Mai Amfani Da Iskar Gas Kirar Gida
El-Rufa’i ya ce ya ɗauki wannan mataki ne a matsayin ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, tare da nufin tallafa wa hukumar ƴansanda wajen tabbatar da ladabi da gaskiya a ayyukansu.
Ya kuma buƙaci hukumar ƴansanda da ta gudanar da bincike mai zaman kansa, tare da hukunta duk jami’in da aka samu da laifi.
“Ƙarar ta shafi babban ƴansandan Jihar Kaduna da ake zargi da wannan rashin ƙwarewa,” in ji sanarwar.
El-Rufa’i ya jaddada cewa manufarsa ita ce ganin an tabbatar da gaskiya da bin doka a ƴansandan Nijeriya, domin tabbatar da jami’an suna aiki da gaskiya da biyayya ga ƙa’ida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp