Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta kammala shirin daukar malaman firamare 10,000 domin maye gurbin wadanda aka kora don inganta Karatun daliban jihar.
Mataimakiyar gwamna, Dakta Hadiza Balarabe ce ta bayyana haka a Kaduna, a ranar Laraba, a wajen kaddamar da rabon kayayyakin koyon karatu ga dalibai a makarantun firamare na gwamnati 4,260 da kuma cibiyoyin koyarwa 838.
A ranar 19 ga watan Yuni ne gwamnatin jihar ta sanar da korar malaman makarantun firamare 2,357 saboda rashin cin jarabawar da gwamnatin ta gudanar.
A shekarar 2018 gwamnatin jihar ta kori Malamai 21,780, saboda, acewarta sun fadi jarabawa, sannan kuma ta sake korar Malamai 233 a watan Disambar 2021 bisa zarginsu da amfani da takardun shaidar Karatu na bogi.
Mataimakiyar gwamnan ta ce gwamnati za ta ci gaba da tantance malaman da ba su cancanta ba a makarantun gwamnati kuma babu wani abin da zai hana yin hakan.