Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya (CDS), Janar Luck Irabor, ya tabbatar wa iyalan fasinjojin jirgin da aka sace daga Abuja zuwa Kaduna, cewar ‘yan uwansu za su kubuta.
Ya kuma ce za a damke wadanda suka yi garkuwa da su a kuma gurfanar da su a gaban kotu.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda A Ribas
- 2023: Bayan Buhari, Dole Dan Kudu Ya Zama Shugaban Kasa – Fayose
Irabor ya bayyana hakan a lokacin wani shiri na gidan Talabijin na AriseNews a ranar Laraba, inda ya ce duk da cewa ‘yan bindigar na amfani da fasinjojin jirgin da suka sace a matsayin garkuwa, jami’an tsaro za su ci gaba da gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarda ba don ganin an ceto su.
Irabor ya ce, “Abu da yawa na faruwa, gwamnati na yin iya iyawarta. Ina so in tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa duk wadanda aka kama za su kubuta kuma za a gurfanar da wadanda ke da hannu wajen aikata laifin a gaban Kuliya.”
Idan za a iya tunawa a watan Maris 2022 ne, wasu ‘yan ta’adda suka dasa wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna bam, inda ya kashe mutane tara sannan wasu suka samu rauni.
‘Yan ta’addan sun sace wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasan, inda suke ci gaba da tsare su bayan sakin wasu daga cikinsu.