Daga karshe dai Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Wakilai da ke kula da harkokin babban bankin kasa da kuma bankuna dangane da sabon tsarin sauya fasalin kudade da daina amfani da tsofaffin takardun kudade.
Majalisar ta tura wa Emefiele sammaci kan rikita-rikitar ta biyo bayan sauya fasalin manyan takardun kudade da kuma sauya tsofaffin takardun kudi zuwa sabbi.
- Ya Kamata Mutane Su Yi Amfani Da Kwanaki 10 Wajen Mayar Da Tsofaffin Kudinsu Banki – Sanusi
- Tsohon Shugaban Jam’iar Bayero Ta Kano, Farfesa Ibrahim Umar Ya Rasu
Emefiele ya gurfana a gaban Kwamitin wucin gadi da Majalisar ta kafa da aka daura wa alhalin bincikar rikicin da ke karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado-Doguwa a yau Talata.
Idan za a iya tunawa dai shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a makon da ta gabata ya yi barazanar bada umarnin kama Emefiele muddin ya ki bayyana a gaban Majalisar zuwa ranar Talata.
Wannan matakin ya biyo bayan shure gayyata har kusan sau hudu da Majalisar ke aike wa Emefiele.
Da ya ke bayani a gaban kwamitin, Mista Godwin Emefiele, ya shaida wa duniya cewa, bankunan kasuwanci za su ci gaba da karbar tsofaffin kudade har bayan karewar wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudade da bankin CBN din ya umarta zuwa ranar 10 ga Fabrairun 2023.
Kodayake Godwin ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke kawo nakasu ga tsarin sauya fasalin kudin musammman a bankuna duk da umarnin da CBN ya baiwa bankunan. Ya na mai cewa, sun nemi taimakon hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da sauran hukumomin tsaro domin dakile aniyar masu janyo zagon kasa.
Ya ce tsarin takaita kudade na da matukar tasiri wajen hana hauhauwar farashin kayayyaki da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya ce, alfanun sauya kudin nan na da yawa sosai domin hatta masu garkuwa da mutane za su rasa hanyoyin cin karensu babu babbaka.
Ya nemi ‘yan Nijeriya da su Kara hakuri kan wahalar da suke fuskanta musamman na wahalar samun takardun sabon kudin, ya ce nan gaba kadan komai zai daidai.
Ya kara da cewa CBN ya tura ma’aikatan na musamman guda 30,000 yankunan karkara da ka iya fuskantar wahalhalu game da sauya tsofaffin kudadensu.