Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya sake gurfana a gaban babbar kotun jihar Legas, kan wasu sabbin zarge-zarge 26 ciki har da zargin karkatar da wasu biliyoyin kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.
Emefiele, tare da Henry Isioma Omole, za sun gurfana a gaban mai shari’a Rahman Oshodi na babbar kotun Ikeja a ranar Litinin da wasu sabbin tuhume-tuhume.
- Mayakan Boko Haram Sama Da 200,000 Sun Ajiye Makamansu – Gwamnatin Borno
- Jami’an Tsaro Sun Dakile Harin ‘Yan Bindiga Na Fasa Rumbun Ajiyar Kayan Abinci A Katsina
Tuhume-tuhumen masu lamba ID/23787c/2024, an shigar da tuhume-tuhumen a ranar 3 ga watan Afrilu, 2024, inda EFCC ta yi zargin cewa Emefiele ya ci zarafin ofishinsa daga 2022 zuwa 2023.
EFCC ta kuma yi zargin cewa tsohon gwamnan na CBN ya karkatar da sama da dala biliyan biyu ba bisa ka’ida ba