Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya musanta tuhumar da ake masa a gaban babbar kotun tarayya, da ke Abuja.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Maryan Anenih, bisa zargin amincewa da buga Naira Miliyan 684.5 kan kudi Naira biliyan 18.96.
- ‘Yansanda Sun Kama Matashin Da Ya Cinna Wa Masallaci Wuta A Kano
- Matashi Ya Banka Wa Masallaci Wuta Yayin Da Ake Sallah A Kano
EFCC ta zargi Emefiele da karya doka ta hanyar aiwatar da manufar sauya Naira ta gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda hakan ya jefa jama’a da dama cikin halin ni ‘yasu.
An kuma tuhumi tsohon gwamnan na CBN da amincewa da cire Naira biliyan 124.8 ba bisa ka’ida ba daga asusun tattara harajin tarayya.