Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce, umarnin da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar a kan lokaci na rage haraji kan muhimman kayayyakin abinci da ake shigowa da su kasar ya haifar da faduwar farashin kayan abinci a fadin kasar nan.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Alhamis, BUA, ya bayyana cewa, rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci da aka yi a shekarar da ta gabata, ya bai wa manyan masu sarrafa abinci irin su BUA damar shigo da shinkafa, masara, alkama, da dawa a daidai lokacin da farashin ya yi tashin gwauron zabi.
- Majalisar Wakilai Za Ta Binciki Yadda Aka Samu Mummunan Sakamakon Jarabawar UTME 2025
- An Kaddamar Da Yankin Gwajin Aikin Gona Da Sin Ta Gina A Zimbabwe
“A lokacin shinkafa ta haura N100,000 kan duk buhu mai nauyin kilo 50, buhun fulawa ya kai kusan N80,000, masara kuma a N60,000,” in ji BUA. “Amma tare da hangen nesa na Shugaban kasa, mun sami damar shigo da kayayyaki masu yawa, mu sarrafa su cikin sauri, wanda hakan ya sanya farashin kayayyakin faduwa warwas.”
A cewarsa, yanzu haka ana sayar da shinkafa kimanin naira 60,000 kan kowane buhu, buhun fulawa kan naira 55,000, da masara a kan Naira 30,000.
Ya yi bayanin cewa, kafin zartar da umarnin rage harajin kwastam kan kayayyakin abinci, ‘yan kasuwa kan sayen kayan abinci tun yana gona su boye, sannan su sayar da shi a farashi mai tsada. Ya kara da cewa, “Amma a yanzu, wannan shirin ya kare, yanzu masu irin wannan halin, asara kawai suke kirgawa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp