Sana’ar jigilar kaya cikin sauri ta kasar Sin ta bunkasa a shekarar nan ta bana, inda kunshin kayayyakin da aka jigila cikin sauri suka zarce biliyan 100 ya zuwa yanzu, adadin da ya yi saurin zarce wanda aka samu a makamancin lokaci na shekarar bara. Kuma hakan ke nuni ga bunkasar sayayyar kayayyaki, da wanzuwar kyakkyawan yanayin tattalin arzikin kasar.
A Talatar nan ne aka cimma alkaluman yawan aikewa da kunshin har biliyan 100, kwanaki 71 kafin cimma wa’adin hakan a shekarar 2023, kamar dai yadda ofishin gidan waya na kasar ko SPB ya tabbatar.
- Kasar Sin: Dawwamammen Ci Gaba Shi Ne Tushen Zaman Lafiya Mai Dorewa A Afrika
- Tinubu Zai Kai Ziyara Equatorial Guinea Ranar Laraba
Bisa wannan adadi, matsakaicin yawan aikewa da kunshin kaya na al’ummar kasar Sin ya kai kusan kunshi 71.43 duk mutum guda, ko kunshin 5,144 a duk dakika daya.
Tuni dai sana’ar jigilar kaya cikin sauri ta Sin ta zamo wata manuniya, ta auna ingancin tattalin arzikin kasar, a gabar da tattalin arzikin kasar ke farfadowa bisa daidaito, kuma sana’ar ta kafa sabon matsayin inganci a manyan sassa guda 3. (Mai fassara: Saminu Alhassan)