An bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama jiya Alhamis a birnin Beijing na kasar Sin. Kuma cikin sakonsa ga taron, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jadadda niyyarsa na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya.
Hakika duniya ta shiga wani yanayi na sauye-sauye da rashin tabbaci da ba a gani ba cikin daruruwan shekaru, daga rikice-rikice da yake-yake zuwa takkadamar cinikayya da yada karairayi, lamarin dake bukatar haduwar mabambanta wayewar kai wajen nazartar bambance-bambancen dake tsakaninsu da lalubo hanyoyin cudanya da juna cikin lumana da girmama juna.
- Sojoji Sun Kama Mutum 2 Da AK-47 A Taraba
- Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
Taron ya zo a kan gaba, domin zai samar da wani dandalin jin ra’ayoyi da zakulo irin rawar da raya wayewar kai zai taka, bisa la’akari da yanayin da duniya da al’ummunta suka tsinci kan su a ciki. Babban tushen rikice-rikice da yake-yake shi ne rashin fahimta da daukar wata al’umma ko kabila ta fi wata daraja. Amma abun fahimta kamar yadda taken wannan taron yake “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya” shi ne, kiyayewa maimakon dakile wayewar kan al’adun bil adama, zai taka rawa gaya wajen warware tarin matsalolin da ake ciki. Kowacce kabila ko al’ada na da nata kyawawan sigogi na musamman dake zaman abun koyo, kuma daukaka su shi ne zai kara karfafa cudanyar mabanbantan al’ummomi da fahimtar asalinsu da ma kara ilimi da wayewar kai a duniya.
Gudana da taron a mahaifar shehun malami na kasar Sin watau Confuscius, wanda ya dabbaka akidar zaman lafiya da lumana tsakanin kasa da kasa zai kara ba mahalarta damar fahimtar wayewar kan al’ummar Sinawa da dalilin da a kullum suke zabar ka’idojin girmama juna maimakon raini da moriyar juna maimakon cin riba daga faduwar wani bangare da kuma adalci da zaman lafiya maimakon babakere da fito na fito ko ta da yake-yake.
Fatan shi ne, yayin da mahalartan suka taho da nasu akidu, za su fahimci na kasar Sin, tare da ganin yadda duka za su hadu, su samar da duniya mai kyakkyawar makoma ta bai daya da zaman lafiya tsakanin mabambantan wayewar kan al’adu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp