Birni ba dajin da aka gina da siminti ba, wuri ne da bil Adama da nau’o’in halittu suke zama a ciki. Kasar Sin ta fidda sabuwar shawarar gina “birnin zamani na al’umma”.
Kwanan baya, kasar Sin ta kira muhimmin taro mai nasaba da biranen kasa, inda aka amince birane suna da rayuwa, ganin yadda suke yin numfashi, da girma, da samun kyautatuwa da kansa. Shi ya sa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fidda shawarar cewa, idan muna son gina biranen zamani na al’umma, ya kamata a mai da matukar hankali kan al’umma, wato a bauta wa al’umma, a dogara kan al’umma wajen gina birane. (Mai Fassara: Maryam Yang)














