Mutanen da yawansu bai wuce kashi 1 cikin dari a duniya ne ba sun samu wadatar arziki da fiye da kashi 60 cikin dari. Yayin da ake fuskantar matsalar gibin dake tsakanin hamshakai da matalauta a duniya, kasar Sin ta samar da gudummawarta wajen daidaita matsalar. Confucius ya taba cewa, abin damuwa shi ne yadda kowa ba ya samun daidaito, amma ba zama da talauci ba. Kana kasar Sin ta kawar da talauci ga mutane miliyan 100 a cikin shekaru 8, kuma a halin yanzu ana kokarin sa kaimi ga dukkan jama’ar kasar su samu wadata tare, yayin da ake kokarin zamanintarwa irin ta kasar Sin. Kasar Sin ba ta bi hanyar kasashen yammacin duniya wacce ta haifar da matsalar gibin dake tsakanin masu arziki da matalauta ba, kuma ta samar da sabuwar hanya ga duk duniya wajen sarrafa harkokin kasar. (Zainab Zhang)













