Yau Talata ita ce ranar cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS. A cikin lokacin sanyi na shekarar 2012, jama’ar kasar Sin sun wayi gari da ganin motocin gwamnati kalilan ne ke kai-komo a kan tituna, kuma an daina amfani da kudin gwamnati wajen shirya liyafar cin abinci a gidajen cin abinci masu tsada, kana hatta kyautar da ake bayarwa ta kek, watau “Mooncake” lokacin bikin tsakiyar kaka an rage girmanta daga dan karamin akwati zuwa wani karamin kunshi.
Wannan shi ne sauyin da aka samu bayan aiwatar da shahararrun “Ka’idoji Takwas” na jam’iyyar JKS. Matakin da aka dauka na dokoki ya zama tamkar wani magani mai karfi wanda ke warkad da “cututtukan” da suka zama matsaloli kamar “sharholiya da kudin gwamnati” wadanda ake ganin ba su taka-kara-sun karya ba amma kuma sannu a hankali suna zubar da kima da martabar jam’iyya mai mulki ta JKS.
Shekaru 13 bayan haka, a lokacin da aka koyar tare da ilmantar da rassan jam’iyyar a dukkan matakai na kasar Sin game da “Ka’idoji Takwas”, wadannan ka’idojin, wadanda tun farko sun mayar da hankali ne kan “magance cin hanci da rashawa tun daga tushe”. Sun tashi daga zama tsarin gina salon gudanar da aiki zuwa gawurtaccen tsarin tafiyar da shugabanci na jam’iyyar.
A karkashin wannan, babban sirrin JKS wajen samun bunkasa da kuma kiyaye nasarar da ta samu a cikin shekaru fiye da dari a tarihi, shi ne juyin juya halin da take yi wa kanta. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp