Faidar Istigfari:
Ibnu Juzai a-Kalbi Allah Ya yi masa rahama yana cewa:
وَ أَمَّا ٱلٱسْتِغْفَارُ فَثَمَرَتُهُ ٱلٱسْتِقَامَةُ عَلَى ٱلتَّقْوَىٰ، وَ ٱلْمُحَافَظَةُ عَلَىٰ شُرُوطِ ٱلتَّوْبَةِ مَعَ إِنْكَارِ ٱلْقَلْبِ بِسَبَبِ ٱلذُّنُوبِ.
Fassara:
“ Ka ga yin istigfari, sakamakonsa shi ne tsayuwa kan taƙawa, da kiyaye sharuɗan tuba, tare da inkarin saɓo da zuciya za ta yi saboda zunuban da aka aikata” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/65]
Fashin Baƙi:
Wannan magana ta Ibnu Juzai al-Kalbi Allah Ya ji ƙan sa tana bayani ne a kan istigfari ( wato nema gafarar Allah) da sakamakonsa a rayuwar mutum. Domin fahimtar wannan tasa dalla-dalla, zan yi bayani a matakai uku:
Ma’anar Istigfari da Muhimmancinsa:
Istigfari na nufin neman gafarar Allah Ta’ala bisa zunubai da aka aikata. Ana yin hakan ta hanyar faɗin “Astaghfirullah” da sauran lafuzza masu kama da hakan. Allah Maɗaukakin Sarki ya yawaita umurni da a yi istigfari a cikin Alƙur’ani, kamar yadda ya ce:
” sai na ce: Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai ywana gafara ne” Suratu Nuh aya ta 10.
Manzon Allah (S.A.W) yana yawaita istigfari fiye da sau saba’in a rana, kamar yadda hadisi ya tabbatar da haka a cikin Sahihul Bukhari da Muslim..
Sakamakon Istigfari a Bisa Maganar Ibnu Juzai:
Ibnu Juzai yana bayani ne cewa istigfari yana da tasiri a rayuwar mai neman gafara, kuma sakamakonsa yana bayyana a cikin:
Tsayuwa Kan Taƙawa:
Taƙawa tana nufin kiyaye umarnin Allah da guje wa haninsa wato nisantar saɓa masa. Idan mutum yana neman gafarar Allah da gaske, hakan yana ƙarfafa tsoron Allah a zuciyarsa, wanda ke hana shi komawa ga zunubi. Allah Ta’ala Yana cewa:” Kuma ku tuba ga Allah gaba ɗayanku ya ku mummunai domin ku rabauta” Suratun Nur aya ta 31.
Kiyaye Sharuddan Tuba:
Tuba tana da sharuɗa guda uku, idan zunubin ba ya da alaƙa da wani bawa, to sharuɗan guda uku ne, idan kuma yana da alaƙa da wani, to sharuɗan hudu ne kamar haka:
1. Nadama bisa abin da aka aikata.
2. Barin zunubin nan take ba tare da jinkiri ba.
3. Ƙudirin kada a koma ga zunubin nan gaba.
4. Idan ya shafi wani mutum, sai a biya shi haƙƙinsa.
Idan mutum yana istigfari ba tare da kiyaye waɗannan sharuɗa ba, to istigfarinsa ba zai ba yi mass tasiri sosai ba.
Inkarin Saɓo da Zuciya:
Wannan yana nuna cewa zuciyar mai istigfari tana ƙin saɓo kuma tana jin haushin zunuban da aka aikata a baya. Wannan na nufin istigfari na gaskiya yan ƙarfafar bawa a kan aibata saɓo da jin nauyin aika shi. Hakan yana nufin istigfari yana gina halin mutumin da ya fahimci girman zunubi, kuma hakan yana hana shi sake aikata shi.
Muhimmancin Wannan Magana a Rayuwa:
Maganar Ibnu Juzai tana koyar da cewa:
• Istigfari ba kawai furuci ba ne, yana da tasiri ga zuciya da hali.
• Dole ne istigfari ya kasance tare da takawa da gujewa sabo.
• Kiyaye sharuɗan tuba yana tabbatar da cewa istigfarin mutum ya dace da shari’a.
A taƙaice, Ibnu Juzai a-Kalbi Allah Ya ji ƙan sa yana jaddada cewa istigfari na gaskiya yana haifar da tsayuwa a kan addini, da kiyaye dokokin Allah, da gujewa komawa ga zunubi. Wannan yana nufin cewa nema gafarar Allah ba wai magana ce ta fatar baki kawai ba, sai da aikin zuciya da na gaɓɓai.
Allah ya sa mu kasance cikin masu istigfari na gaskiya!
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp