• English
  • Business News
Friday, July 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [20]

by Nuhu Ubale Ibrahim
4 months ago
in Addini, Bakon Marubuci, Ilimi
0
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fa’idar Salatin Annabi (S.A.W):

Muhammad ɗan Ahmad ɗan Juzai al-Kalbi Allah Ya haskaka kabarinsa yana cewa:

وَأَمَّا الصَّلَاةُ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ فَثَمَرَتُهَا شِدَّةُ الْمَحَبَّةِ فِيهِ، وَالْمُحَافَظَةُ عَلَى ٱتِّبَاعِ سُنَّتِهِ.

Fassara:

“Amma yin salati ga Annabi (S.A.W) yana haifar da tsananin ƙauna a gare shi, da kuma kiyaye bin sunnarsa” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/64].

Labarai Masu Nasaba

‘Yan Makaranta Sun Kera Mota Mai Amfani Da Lantarki A Sakkwato

An Samu Rarrabuwar Kai Kan Makin Shiga Manyan Makarantu

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18]
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]

Fashin Baƙi:

Maganar Ibn Juzai tana nuni ne ga girman tasirin salatin Annabi (S.A.W)i a rayuwar Musulumi, musamman dangane da ƙaunar Annabi Muhammad (S.A.W) da bin sunnarsa. Domin cikakken bayani kan wannan batu, bari na ɗan zurfafa bincike a cikin abubuwan da ke cikinsa.

Ma’anar Salati
A fagen ilimi, salati ga Annabi (S.A.W) na da fassarori da dama:

Idan Allah ne Yake yin Salati: Yana nufin yabo da ɗaukaka ga Annabi (S.A.W) da Allah Yake yi masa a wajen mala’iku. Idan Mala’iku ne Suka yi Salati: Yana nufin nema wa Annabi (S.A.W) rahama da ɗaukaka, da daraja da martaba a wurin Allah. Idan Musulumi Suka yi Salati: Yana nufin nema wa Annabi (S.A.W) albarka da gafara, da ɗaukakar daraja da girma da matsayi wurin Allah.

Allah Ya barta mana cewa:” Lalle Allah da mala’ikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya ku mummunai! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama mai yawa” Suratul Ahzãbi aya ta 56.

Wannan aya tana nuna cewa yin salati wajibi ne, kuma yana da babbar lada.

Salatin Annabi Yana Kawo Ƙaunar Annabi(S.A.W):

Domin a fahimci wannan batu, sai mu tambayi kanmu: Ta yaya mutum yake ƙaunar wani? Amsa a nan ita ce: Yana ƙaunar wanda yake yawan tunawa ne, kuma yana ƙaunar wanda yake amfana da shi ne a rayuwa, ya kuma ƙaunar wanda yake tare da shi a zuciya. Salati ga Annabi (S.A.W) yana ƙara ƙaunarsa domin Ya na yawan tunatar da Musulumi Annabi (S.A.W).

Yayin da mutum yake yawan yin salati, hakan yana sa zuciyarsa ta cika da tunanin Annabi (S.A.W), har ya zama yana ƙaunar sa fiye da kansa. Annabi (S.A.W) ya bayyana cewa: ”Ɗayanku ba zai zama cikakken mummuni ba har sai na zamnto Ni ne na fi soyuwa a gare sa sama ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.

Salati Yana Jawo Amsawar Annabi (S.A.W):
Annabi (S.A.W) ya ce: “ Babu wani da zai yi min salati face Allah Ya dawo min da ruhina har sai na amsa masa” Hadisi ne ingantacce Abū Dãwūd da Ahmad ne suka ruwaito.

Wannan yana nuna cewa salatin da Musulumi yake yi yana isa ga Annabi (S.A.W), kuma yana jin sa. Idan Musulumi yana da wannan fahimta, tabbas ƙaunarsa ga Annabi (S.A.W) za ta ƙaru.

Salati Yana Ƙara Fahimtar Rayuwar Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati, zai shiga neman ilimi game da halayen Annabi (S.A.W), da maganganunsa da ayyukansa. Wannan zai sa ƙaunarsa ta ƙaru, kamar yadda mutum ke ƙaunar wanda ya san halinsa.

Salati Hanya ce Ta Shiga Aljanna:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Duk wanda ya manta yi min salati, to ya kuskure hanyar shiga Aljanna “ Hadisi ne ingantacce Ibnu Maja ne ya ruwaito. Wannan yana nuna yin salati ga Manzon Allah (S.A.W) hanya ce ɗoɗar ta shiga Aljanna.

Salati Na Sanya Mutum Ruƙo da Sunna:
Bin sunna yana nuna ingantacciyar ƙaunar Annabi (S.A.W). Idan mutum ya san cewa yin salati yana ƙara masa kusanci da shi, zai so yin koyi da shi a aikace. Allah Ya ce:” Ka ce: In kun kasance kuna son Allah, to ku yi min biyayya, sai Allah Ya so ku, kuma Ya gafarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai” Suratu Ãli Imrãn aya ta 31.

Salati Yana Ƙarfafa Son Bin Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati zai fi son yin koyi da Annabi (S.A.W) a cikin salla, da hulɗa da jama’a, da ibada da kuna mu’amala.
Idan mutum yana yawan yin salati, zuciyarsa tana son yin koyi da halayensa na gaskiya, kamar riƙon amana, da tausayi, da sanin ya kamata.

Salati Yana Hana Saɓa wa Annabi (S.A.W):
Duk wanda yake yawan yin salati, zai fi jin nauyin yin saɓo ko barin sunna. Domin yana sane da matsayin Annabi (S.A.W), kuma yana jin nauyin rashin bin hanyarsa.

Salati Yana Kawar da Tsauraran Ƙa’idojin bidi’a:
Yin salati yana hana mutum bin hanyoyin da ba sunna ba. Domin yana sane cewa abin da Annabi (S.A.W) ya bari, shi ne mafi alheri. Matuƙar mutum ya lazimci salatin da Annabi (S.A.W) ya zo da shi, to tabbas zai sami haka.

Fa’idoji Goma na Yin Salati ga Annabi (S.A.W)
-Yin salati yana da fa’idodi masu yawa, daga ciki akwai:
• Allah yana yin salati sau goma ga Musulumin da ya yi salati sau ɗaya.
• Ana gafarta wa mutum zunubi.
Ana ɗaga matsayi a Aljanna.
• Ana samun ceto (shafa’a) a ranar Alƙiyama.
• Ana samun waraka daga damuwa da baƙin ciki.
• Ana samun amsa addu’a.
• Ana kasancewa tare da Annabi (S.A.W) a ranar Alƙiyama.
• Ana samun kariya daga wahalar kabari.
Ana samun albarka a rayuwa.
• Ana samun kwanciyar hankali da soyayya a zuciya.

Hanyoyin yin salati suna da yawa, amma mafi inganci shi ne wanda Annabi (S.A.W) ya koyar, wato Salatin Ibrahimiyya
“Allahumma salli ‘ala Muhammadin wa ‘ala ali Muhammadin, kama sallaita ‘ala Ibrahima wa ala ali Ibrahima, innaka hamidun majid. Allahumma barik ala Muhammadin wq ala Ali Muhammadin kama barakta ala Ibrahim wa ala Ali Ibrahim innaka hamidun majid.”

A taƙaice, wannan magana ta Ibn Juzai tana nuni ne ga cewa wanda yake yawan yin salati ga Annabi (S.A.W) zai ƙara ƙaunarsa kuma zai fi son bin sunnarsa. Idan muna son Annabi (S.A.W), dole ne mu yawaita yin salati gare shi. Idan muna son bin sunnarsa, dole ne mu yawaita tunawa da shi. Idan muna son rabauta a duniya da lahira, salati na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da za su kai mu ga hakan. Allah Ta’ala Ya sa mu kasance cikin masu yawan salati ga Annabi (S.A.W) da bin sunnarsa har mu kasance tare da shi a Aljanna!. Amin.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abu Razina Nuhu Ubale PakiAl-qur'aniAlƙur’aniIbnu JuzaiRamadanTafsiriTafsirin Alƙur’aniTafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu

Next Post

Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya

Related

‘Yan Makaranta Sun Kera Mota Mai Amfani Da Lantarki A Sakkwato
Ilimi

‘Yan Makaranta Sun Kera Mota Mai Amfani Da Lantarki A Sakkwato

6 days ago
UTME
Ilimi

An Samu Rarrabuwar Kai Kan Makin Shiga Manyan Makarantu

6 days ago
Jami’ar Ilorin Ta Karrama Shugabannin JAMB, THISDAY Da Wasu 63 A Bikin Shekara 50
Ilimi

Jami’ar Ilorin Ta Karrama Shugabannin JAMB, THISDAY Da Wasu 63 A Bikin Shekara 50

6 days ago
Ƴansanda Sun Kama Ɗalibai 11 Kan Kisan Wasu Ɗalibai 2 A Kano
Ilimi

Ƴansanda Sun Kama Ɗalibai 11 Kan Kisan Wasu Ɗalibai 2 A Kano

1 week ago
Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya
Ilimi

Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya

1 week ago
An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano
Ilimi

An Fara Binciken Mutuwar Wasu Ɗalibai 2 A Makarantar Kwana A Kano

1 week ago
Next Post
Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya

Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Lawal Ya Yi Ta’aziyyar Sarkin Katsinan Gusau

Gwamna Lawal Ya Yi Ta’aziyyar Sarkin Katsinan Gusau

July 25, 2025
Manzon Allah

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)

July 25, 2025
‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli

‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli

July 25, 2025
Shugaban Hukumar DSS Ya Kaddamar Da Cibiyar Koyar Da Addinin Musulunci A Kaduna 

Matsalar Tsaro: Sarakuna Sun Bukaci Gwamnati Ta Canza Salo

July 25, 2025
Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU

Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU

July 24, 2025
Buƙatar Rijistar Sabbin Jam’iyyu Ta Kai 144 — INEC

Buƙatar Rijistar Sabbin Jam’iyyu Ta Kai 144 — INEC

July 24, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI 

Firaministan Sin Zai Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI 

July 24, 2025
Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato

Sojoji Sun Kwato Makamai Daga Hannun Ƴan Bindiga, Sun Ceto Yaro A Filato

July 24, 2025
Alakar Sin Da EU Na Bukatar Hadin Gwiwa Ba Raba-gari Ba

Alakar Sin Da EU Na Bukatar Hadin Gwiwa Ba Raba-gari Ba

July 24, 2025
Binciken CGTN: Masu Bayyana Raayoyi Na Turai Sun Gamsu Da Moriyar Cinikayya Tsakanin Sin Da Turai Sama Da Ta Turai Da Amurka

Binciken CGTN: Masu Bayyana Raayoyi Na Turai Sun Gamsu Da Moriyar Cinikayya Tsakanin Sin Da Turai Sama Da Ta Turai Da Amurka

July 24, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.